'Yan Hisbah sun kama mabarata 262 a Kano

'Yan Hisbah sun kama mabarata 262 a Kano

Hukumar Hisabha ta jihar Kano ta ce ta kama mutane 262 da ake zargin mabarata ne a watan Augusta a birnin Kano saboda saba dokar haramta bara da aka kafa a jihar.

Mai magana da yawun hukumar ta Hibah, Lawan Ibrahim ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a Kano cewa wadanda aka kama sun hada da manya 175 da yara 87.

Ibrahim ya ce an kama mabarantan ne yayin sumame da jami'an hukumar suka yi a sassa daban-daban na birnin Kano kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce anyi kamen a Ajasa road, Lodge road, Kantin Kwari, Railway, Sabon gari da State road.

DUBA WANNAN: Gwamna Makinde ya nada 'yan jam'iyyun hamayya biyu a matsayin hadimansa

Ibrahim ya ce, "262 cikin mabaratan 'yan Kano ne, 158 sun fito daga jihohin Bauchi, Katsina, Sokoto Borno da Jigawa yayin da biyu kuma 'yan Ghana ne sannan biyu kuma 'yan Nijar ne."

Ya kara da cewa mutune uku cikin mabaratan suna fama da tabin hankali.

Ya yi bayanin cewa dukkan wadanda ba 'yan jihar Kano bane za a mayar da su jihohinsu.

Ibrahim ya ce wadanda kuma 'yan Kano ne za a tantance su sannan a basu shawarwari kafin daga bisani a sake su saboda dukkansu wannan ne karo na farko da suka aikata laifin.

Ya roki mabaratan suyi amfani da hannunsu domin yin sana'o'in domin inganta rayuwansu da kare mutuncinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel