Da zaran ka iya karatu, rubutu, da fahimta, toh kana iya tsayawa takarar zabe – Tanko Yakassai

Da zaran ka iya karatu, rubutu, da fahimta, toh kana iya tsayawa takarar zabe – Tanko Yakassai

Wani babba jigon arewa, Alhaji Tanko Yakassai ya bayyana cewa ba abun mamaki bane gare shi ganin hukucin da kotun da ke sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yake, inda ta tabbatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta gabatar.

Alhaji Tanko yayin da yake mayar da martani akan hukuncin kotun zaben ta wayar talho a jihar Kano a daren Laraba, yace: “ban ji mamaki ba. Hukuncinta bai zo mun a bazata ba.”

Tsohon dan siyasan ya bayyana cewa tunanin shi game da kotun sauraron kararrakin zabe a matakin shugaban kasa shine cewa basu sauya ba kuma ba za su sauya sakamakon zaben shugaban kasa ba a Najeriya.

Sabanin haka, ya yabi yanayin yanda suka kwance suka kuma warware al’amuran da suka shafi zaben, maimakon dunkule su waje guda ba tare da warware kullin ba.

KU KARANTA KUMA: Toh fah: Ana shigo da muggan makamai cikin Najeriya – Babban mai ba kasa shawara kan tsaro

Ya kuma lura cewa hukuncin ya kawo karshen lamarin takardar shaidar karatu a mizanin tsayawa takarar zabe a Najeriya, inda ya kara da cewa a cewar kotun zaben, "da zaran ka iya karatu da rubutu da kuma fahimtar abunda ake fadi, toh hakan naa nufin ka mallaki satifiket din makarantar sakandare sannan kana iya tsayawa takarar zabe a kowani mataki."

Da aka tambaye shi ko yana ganin sansanin Atiku Abubakar za ta daukaka kara akan hukuncin, yace: "Ban hadu da su a; ban sani ba, amma mu jira mu gani."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel