NAF ta tarwatsa sansanin bayar da horo na Boko Haram a Borno

NAF ta tarwatsa sansanin bayar da horo na Boko Haram a Borno

Rundunar Sojojin Saman Najeriya (NAF) ta lalata sansanin bayar da horo na kungiyar ta'addanci ta Islamic State of West Africa Province (ISWAP) da ke kusa da Mallam Fatori a iyakar Tafkin Chadi da ke arewacin jihar Borno.

Mai magana da yawun NAF, Air Commodore Ibikunle Daramola ne ya tabbatar da afkuwar hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a a babban birnin tarayya, Abuja.

Daily Trust ta ruwaito cewa Daramola ya ce dakarun sojojin sama (ATF) na Operation Lafiya Dole ne suka yi nasarar lalata sansanin 'yan ta'addan.

Ya yi bayanin cewa an kai harin ne bayan samun bayyanan sirri masu inganci ta aka tabbatar ta hanyar amfani da na'urar leken asiri da ISR.

DUBA WANNAN: Buhari zai tsamar da mutum miliyan 10 daga talauci a shekara 10 – Osinbajo

Daramola ya ce na'urar ta ISR ta gano wani gini a cikin wani tsibiri da ke Tafkin Chadi da 'yan ta'addan ke amfani da shi domin horas da sabbin mayaka.

Ya ce, "Hakan yasa ATF ta aike da jiragen yaki wurin kuma bayan sun isa wurin suka tabbatar akwai 'yan ta'adda a cikin gidan.

"Jirgin yakin ya yi wa ginin luguden wuta inda ya lalata shi tare da kashe 'yan ta'addan da ke ciki.

"An kuma sake yi wa tsirarun 'yan ta'addan da suke tsere daga ginin luguden wuta."

Mai magana da yawun na NAF ya ce rundunar za ta cigaba da aikin da ta ke yi na kakkabo sauran 'yan ta'addan da ke yankin Arewa ta Gabas tare da hadin gwiwar sauran jami'an tsaro na kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel