Buhari zai tafi Burkina Faso domin halartar taron ECOWAS a ranar Asabar

Buhari zai tafi Burkina Faso domin halartar taron ECOWAS a ranar Asabar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi birnin Ouagadougou da ke Burkina Faso a ranar Asabar domin hallartan taron shugabanin kasashe na ECOWAS da kuma taro na musamman kan yaki da ta'addanci.

Shugabanin kasashen Afrika ta Yamma sun kira taron ne domin bita kan matakan da suka dauka kan yaki da ta'addanci kawo yanzu domin sanin matakan da za su dauka don inganta yaki da ta'addancin duba da cewa matsalar na karuwa.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya ce shugabanin kasashen sun yanke shawarar yin taron ne yau na yayin taro karo na 55 na shugabanin ECOWAS da aka yi a ranar 29 ga watan Yuni a Abuja kamar yadda muka samu daga Daily Trust.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari ya yi na'am da hadin kai wurin yaki da ta'addanci kuma zai cigaba da hadin gwiwa da kasashen ECOWAS da sauran kungiyoyin kasa da kasa domin magance matsalar.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa nafi gamsuwa da bawa mata rikon amanar kudin Najeriya - Buhari

A taron da za a gudanar a Ouagadougou ana sa ran shugabanin na ECOWAS za su cimma matsaya kan shirin yaki da ta'addancin tare da sanya ido kan yadda za a kaddamar da shirin domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Wadanda za su yi wa shugaban kasar rakiya sun hada da Gwamn Abubakar Bello na jihar Neja, Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, Okezie Ikpeazu na jihar Abia da kuma Ministan Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama da Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai murabus).

Sauran 'yan tawagar shugban kasar sun hada da Mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, Manjo Janar Babagana Monguna (murabus) da Shugaban Hukumar tattara bayanan sirri (NIA), Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.

Ana sa ran shugaban kasar zai dawo Abuja da zarar an kammala taron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel