Abba gida-gida ya karyata rahoton cewa ya yabawa Buhari

Abba gida-gida ya karyata rahoton cewa ya yabawa Buhari

A wani tsokaci daga kungiyar magoya bayan dan takaran gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, a shafin ra'ayi da sada zumunta na Tuwita, an bayyana cewa dan siyasan ya yabawa umurnin shugaba Buhari na ginin layin dogo daga Ibadan zuwa Kano.

Amma a martanin daya daga cikin masu magana da yawunsa, Ibrahim Adam, shafin Facebook, ya bayyana cewa shahrarren dan siyasan bai furta hakan ba.

Yace: "Wannan ba gaskiya bane kuma Injiniya Abba Kabir Yusuf, bai fadi hakan a shafinsa ba."

A jiya mun kawo muku rahoton cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ya bada daman amfani da kudi dala biyan biyar da rabi wajen ginin layin dogon garin Ibadan zuwa birnin Kano.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 12 ga watan Satumba, a taron masu ruwa da tsaki a sashen arzikin ruwa.

KU KARANTA: Hukumar zabe mai zaman kanta za ta zabge 'yan takara saboda karancin shekaru

Yace: "A jiyan nan, an bada damar gina layin dogon Ibadan zuwa Kano na kudi $5.3bn. Hakazalika mun nemi a bamu kudi domin gina layin dogon Port Harcourt zuwa Warri."

Hakazalika shirye-shirye sun yi nisa don fara sayar da tikitin shiga jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja a shafukan yanar gizo don kauce ma badakalar da ake samu a tashoshin jirgin, wanda hakan ke janyo rikici tsakanin matafiya da jami’an

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel