Ya yi garkuwa da kansa don damfarar mahaifinsa

Ya yi garkuwa da kansa don damfarar mahaifinsa

- Hukumar 'yan sandan birnin tarayya ta cafke wani mutum da take zargi da garkuwa da kansa

- Ya yi hakan ne don ya damfari mahaifinsa kudin fansa

- Ya bayyana cewa bukatar kudi ce matsananciya ta samesa shiyasa yayi hakanhakan

Hukumar 'yan sandan yankin birnin tarayya ta kama wani dan shekaru 35 a duniya mai suna Hamza Abdullahi akan zarginsa da shirya garkuwa da kansa.

Kamar yadda 'yan sandan suka sanar, wanda ake zargin ya shirya garkuwa da kansa don damfarar mahaifinsa.

Bayan shirya garkuwar da kansa, wanda ake zargin da abokansa sun kira mahaifinsa da bukatar N500,000 a matsayin kudin fansa.

Mataimakin kwamishinan 'yan sandan yankin, DCP Sunday Babaji, yayi bayanin yadda suka kama wanda ake zargin: "Yan sanda sun kama wani Hamza Abdullahi da abokinsa Auwalu Shuaibu akan shirya garkuwa da shi tare da bukatar kudin fansa daga mahaifinsa."

"Wanda ake zargin, ya so amfani da hakan ne don samun kudi daga mahaifinsa. An kamasu ne a Katampe bayan da suka je daukar kudin fansan."

KU KARANTA: Toh fah: Ta sace yaro daga gidan marayu tare da siyar da shi

A hirar da yayi da jaridar The Nation akan yadda ya shirya garkuwa da kansa, Abdullahi wanda injiniya ne, yace: "An kama ni ne bayan da na shirya garkuwa da kaina don karbar kudin fansa daga mahaifina. Na shirya hakan ne sakamakon tsananin bukatar kudi da nake."

"Nayi magana da abokina inda na rokesa da ya kira mahaifina ya sanar da shi anyi garkuwa da ni amma zan boye a gidansa. Abokina yayi yadda nace inda ya bukaci N500,000 a matsayin kudin fansa. Ya yi kuma barazana ga mahaifina cewar zai illata ni matukar ba a kawo kudin akan lokaci ba."

"Yayin da ake cinikin, ina boye a Katampe. A ranar da mahaifina yazo kawo kudin fansa, 'yan sandan da mahaifina sun ganeni. Akwai yuwuwar mahaifina ya nuna musu hotona tunda daya daga cikin 'yan sandan ya ganeni."

Da aka tambayesa dalilin damfarar, sai yace: "Ina bukatar kudin ne don biyan kudin haya da wasu abubuwan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel