Toh fah: Ana shigo da muggan makamai cikin Najeriya – Babban mai ba kasa shawara kan tsaro

Toh fah: Ana shigo da muggan makamai cikin Najeriya – Babban mai ba kasa shawara kan tsaro

Babban mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Babagana Mungono, a jiya Alhamis, 12 ga watan Satumba, ya bayyana cewa ana shigo da muggan makamai cikin Najeriya ta iyakokin kasar.

Da yake magana a Lagas a wajen kaddamar da sabbin bindigogin jiragen ruwa biyu da hukumar kwastam na Najeriya tayi a wajen kera jiragen ruwan rundunar sojin ruwa, yace yan Najeriya da dama sun mutu sakamakon muggan makamai da ake fasa kaurinsu.

Yace gwamnatin tarayya ba za ta saduda ga kowani bita da kulli ko matsin lamba daga kowacce kungiya ko mutane ba akan lamarin rufe iyakokin kasar kan kasuwancinsu ba.

A cewarsa, wasu kasashe da ke makwabtaka da kasar sun mara wa gwamnatin tarayya baya kan yadda za a tabbatar da tsaron iyakokin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Sanata Musa ya koka kan wata babban matsala da ke ciwa al'ummar mazabarsa tuwo a kwarya

Munguno yace Operation Swift Response da ke gudana yanzu haka a iyakokin kasar na samun nasara sosai, inda ya bayar da tabbacin cewa gwamnati ta jajirce domin tallafa wa dukkanin hukumomin tsaro domin basu damar yin maganin duk wasu da ke da hannu a fasa kauri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel