Tsaro: An kama barayin shanu a Kano, an kwato shanu 1000 daga hannunsu

Tsaro: An kama barayin shanu a Kano, an kwato shanu 1000 daga hannunsu

Jami'an tsaro karkashin Operation Puff Adder na Rundunar 'yan sandan Najeriya da ke jihar Kano sun kwato sama da shanu 1000 daga hannun wasu mutane uku da ake zargin barayin shanu ne a sumamen da suka kai a dajin Falgore da ke karamar hukumar Doguwa na jihar.

Kwamishinan 'Yan sanda na jihar, Ahmed Iliyasu ya shaidawa manema labarai a ranar Juma'a cewa an samu wannan nasarar ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar Miyetti Allah kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce wadanda ake zargin sun kware wurin fashi da makami da garkuwa da mutane kuma suna daga cikin bata garin da suka dade suna adabar al'ummar garuruwan da ke kusa da dajin Falgore da matafiya.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa nafi gamsuwa da bawa mata rikon amanar kudin Najeriya - Buhari

Ya ce wadanda ake zargin sun hada da Sa'idu Abdullahi mai shekaru 23 daga karamar hukumar Soba na jihar Kaduna, Suleiman Abdullahi da Lawan Mohammed dukkansu 'yan asalin kauyen Damu da ke karamar hukumar Kubau na jihar Kaduna.

Ya cigaba da cewa an kwato bindigu kirar AK 47 biyu da wasu bindigu uku da alburussai 110 daga hannun wadanda ake zargin.

Ya ce jami'an tsaro suna cigaba da bin sahun sauran 'yan kungiyar fashi da makamin da suka tsere da niyyar kwato sauran shanun da makamai da ke hannun su.

CP Iliyasu ya sake jadada cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wurin ganin cewa an kawar da masu aikata laifuka a Kano inda ya ce, "jihar ba mafakan miyagu bane sai dai wurin da za su gamu da ajalinsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel