Hukuncin kotun zabe: PDP ta bukaci Lai Mohammed da sauran mutane da kada su nuna zakewa wajen murna tukuna

Hukuncin kotun zabe: PDP ta bukaci Lai Mohammed da sauran mutane da kada su nuna zakewa wajen murna tukuna

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi kira ga ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, da ya yi hankali wajen murnar hukunci kotun zaben Shugaban kasa.

A wani jawabi daga babban sakataren labaranta, Kola Ologbondiyan, a ranar Alhamis, 12 ga watan Satumba, jam’iyyar tace nan gaba kadan za a datse murnar masu farin ciki da hukunin kotun.

Mista Mohammed ya bukaci PDP da ta ba yan Najeriya hakuri akan janye hankalin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da tayi da karar zabe, maimakon sake daukaka kara akan hukuncin kotun zaben.

Da take martani ga furucin ministan, PDP tace lallai hukucin ya kasance “rashi adalci kai tsaye” wanda ba zai yi tasiri ba a kotun koli.

Jam’iyyar adawar ta jadadda cewa tana da isasshen hujja akan Shugaba Buhari da jam’iyyar APC, da zai sa ta nasara a kotun koli.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa ba a saki Naziru Sarkin waka daga gidan yari ba – Lauyan sa

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamnan jihar Ribas, Mista Nyesom Wike, ya bayyana dalilansa da suka sa ya taya shugaban kasa, Muhammadu Buhari, murnar samun nasara a kotun sauraron korafi a kan zaben shugaban kasa.

Gwamnan ya bayyana dalilan nasa ne ranar Alhamis yayin da ya ke gabatar da jawabi domin kare kansa daga sukar da yake sha a wurin wani taro da ya halarta a Emohua.

Masu sukar gwamna Wike na ganin bai yi wa jam'iyyarsa PDP da dan takarar ta kara ba ta hanyar gaggauta taya Buhari murnar samun nasara a kotu.

A cewar gwamnan, gara ya taya Buhari a bainar jama'a a kan ya kai masa ziyara gida a sirrance cikin dare domin taya shi murna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel