Gwamna Makinde ya nada 'yan jam'iyyun hamayya biyu a matsayin hadimansa

Gwamna Makinde ya nada 'yan jam'iyyun hamayya biyu a matsayin hadimansa

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya nada 'yan jam'iyyun hamayya biyu a matsayin hadimansa kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

A ranar Alhamis, Mista Makinde ya amince da nadin dan takarar gwaman na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Bolaji Ayorinde a matsayin mai bashi shawara na musamman.

Kazalika, ya kuma nada wani jigo na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) kuma dan takarar majalisar wakilai na tarayya na mazabar Akinyele/Lagelu a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, Yemi Aderibige a matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin kananan hukumomi da sarautun gargajiya.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa nafi gamsuwa da bawa mata rikon amanar kudin Najeriya - Buhari

An bayyana nadin ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yadda labarai na gwamnan, Taiwo Adisa kamar yadda muka samu daga Premium Times.

Wasu nade-naden da ke cikin sanarwar sun hada da nadin Wale Onaolapo a matsayin shugaban Oyo State Security Trust Fund.

An kuma nada tsohon ma'aikacin Jami'ar Ibadan, Gboyega Badejo a matsayin Direkta Janar na tsare-tsare na gwamnan.

Mista Ayorinde dan tsohon alkalin alkalai ne na jihar Oyo, Timothy Ayorinde.

Ya fara karatunsa na aikin koyon aikin lauya a 1983 a Jami'ar Oxford kuma daga bisani ya tafi Jami'ar Landan a 1985 ya yi digiri a 1985 kafin daga daya ya dawo Najeriya ya tafi makarantan lauyoyi da ke Legas.

Ya kafa kamfaninsa na aikin lauya a 1990 sannan ya samu mukamin SAN a 2005.

Ya rike wasu mukamai daban-daban a baya kuma ya yi aiki a kwamitocin gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel