Sanata Musa ya koka kan wata babban matsala da ke ciwa al'ummar mazabarsa tuwo a kwarya

Sanata Musa ya koka kan wata babban matsala da ke ciwa al'ummar mazabarsa tuwo a kwarya

Sanata Mohammed Sani Musa mai wakiltan Gabashin Neja a jiya Alhamis ya koka kan hare-haren da 'yan ta'adda ke kaiwa al'ummar mazabarsa.

The Punch ta ruwaito 'yan ta'addan sun kashe kashe mutane 39 a hare-haren da suka kai a garuruwa 14 da ke jihar ta Neja.

A sanarwar da ya fitar a Minna, sanatan ya koka kan halin da mazabarsa ke ciki inda ya roki gwamnatin tarayya ta aike da jami'an tsaro cikin gaggawa domin kawo karshen fitinar.

'Yan bindigan sun kaiwa wasu garuruwa biyar a kananan hukumomin Rafi da Shiroro hari a cikin kwanaki buyar da suka gabata.

Sanatan ya ce hare-haren ya sanya mazauna kauyukan yin hijira daga gidajensu.

DUBA WANNAN: Kama Naziru sarkin waka: 'Yan Kannywood sun mayar da martani

Ya yi kira ga kwamishinan 'yan sanda da sauran shugabanin hukumomin tsaro su kafa wata tawagar hadin gwiwa ta musamman domin magance matsalar.

Ya kuma shawarci hukumomin tsaron suyi bincike domin gano ko akwai wasu mazauna kauyukan da ke hada baki da 'yan ta'addan domin a kama su.

'Yan ta'adda sun kashe mutane 39 a hare-haren da suka kai a wasu garuruwa 14 da ke kananan hukumomin Rafi da Shiroro yayin da wasu mutane 2,800 sun rasa muhallansu.

Kididdigar da jami'an gwamnati su kayi ya nuna cewa mutane 38 aka kashe yayin da wasu 2,000 suka rasa muhallansu a hare-haren da aka kai a Kwaki, Barden-Dawaki, Ajatawyi, Gwassa, Ajayin, Baton da Giji a karamar hukumar Shiroro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel