Awanni kadan da dawowar 'yan Najeriya, 'yan kasar Afrika ta Kudu sun koma kashe 'yan Pakistan

Awanni kadan da dawowar 'yan Najeriya, 'yan kasar Afrika ta Kudu sun koma kashe 'yan Pakistan

- Sa'o'i kadan da wasu daga cikin 'yan Najeriya suka samu nasarar dawowa gida Najeriya daga kasar Afrika ta Kudu

- Yanzu haka dai mun samu rahoton cewa 'yan kasar sun koma kaiwa 'yan kasar Pakistan hari, suna shiga shagunansu suna kwashe musu kaya

- Wani bidiyo da yake ta yawo a kafar sadarwa ya nuna yadda 'yan Pakistan din suka fara rikici da wasu 'yan Afrika ta Kudu a lokacin da suke debe musu kaya a shago

Wani bidiyo da ya yadu a shafukan sadarwa, ya nuna lokacin da wasu 'yan kasar Pakistan suka fara fada da 'yan kasar Afrika ta Kudu a lokacin da suka kawo musu hari zasu debe musu kayan shago.

An hango wasu 'yan kasar Afrika ta Kudun a lokacin da suka dauki kayayyaki daga shagunan 'yan Pakistan din, wanda aka kawo musu hari basu ji ba basu gani ba a ranar Larabar nan 11 ga watan Satumba.

Yayin da shi kuma daya daga cikin 'yan Pakistan din yaga abin nasu yayi yawa ya yanke hukuncin daukar mataki, inda aka nuno shi yana dukan daya daga cikin masu daukar masa kayan.

KU KARANTA: Mahaifina ya tsine min saboda naki yarda da mijin da ya zaba mini

Haka kuma bidiyon ya nuna wani jami'in dan sanda wanda yake tsaye a wajen amma ya kasa yin komai akan lamarin. Haka sauran masu shaguna da suke makwabtaka da dayan sun kawo masa dauki inda suka fara dukan mutumin, a lokacin ne shi kuma dan sandan ya shiga fadan.

Da yake magana a jiya Alhamis 12 ga watan Satumba, kakakin hukumar 'yan sandan kasar Brig. Leonard Hlathi ya ce sun kama mutane uku da suke da hannu a wannan lamarin, sannan kuma ya bayyana cewa an kwato wasu daga cikin kayayyakin da mutanen suka diba a shagunan mutaanen.

Ya bayyana cewa a yanzu haka dai komai ya dawo daidai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel