Akwai yiwuwar kotun koli ta tisa keyar wasu tsoffin 'yan majalisa uku gidan kaso

Akwai yiwuwar kotun koli ta tisa keyar wasu tsoffin 'yan majalisa uku gidan kaso

- Akwai yuwuwar kotun koli ta iza keyar wasu tsoffin mahukunta uku gidan kaso

- Kotun koli ta kwace kujerunsu tare da bukatar su maidawa majalisar dattawa kudaden da suka karba a matsayin albashi da alawus

- A halin yanzu shekaru biyu kenan amma tsoffin mahukuntan sun yi shiru

Akwai yuwuwar kotu ta tura wasu tsoffin mahukunta uku gidan kaso sakamakon kin biyayya ga hukuncin kotun koli. Kotun koli ta basu umarnin maida wasu kudade ga majalisar dattawa.

A shekarar 2017, kotun ta yanke hukunci ga tsohon sanata Abubakar Danladi, Her men Hembe da Sopuluchukwu Ezeonwuka, dukkansu 'yan majalisar wakilai a lokacin.

A hukunci daban-daban da kotun kolin ta yanke, ta kwace kujerun kowannensu tare da umartarsu da maida albashin da kuma alawus da suka karba yayin da suke majalisar.

Amma kuma, shekaru biyu bayan yanke musu hukuncin, babu daya daga cikinsu da yayi biyayya.

Duk da majalisar dattawa ta ki sakin bayanin cewa sun maida kudaden ko a'a, majiya masu yawa sun tabbatar da cewa tsoffin mahukuntan sun ki bin umarnin kotun.

A jimilla, 'yan siyasan zasu maida Naira miliyan 62 ne ga asusun gwamnatin.

Sopuluchukwu Ezeonwuka: shine kotun kolin ta fara kwace kujerarsa a lokacin yana Dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar mazabar Orumba ta arewa da Anambra ta kudu.

Mahukuncin yayi watanni 22 a majalisar kafin kotu ta sallamesa tare da maye gurbinsa da Ben Nwankwo.

Bayan karbar kujerarsa ne aka umarcesa da ya dawo da kudaden da ya karba a matsayin albashi da alawus wanda sun mai Naira 17,469,870.

Herman Hembe: watanni biyu bayan shari'ar Sopuluchukwu, kotun kolin ta kara kwace kujerar wani Dan majalisar wakilai, Herman Hembe. An maye gurbin Hembe ne da Dorathy Mato wacce ta wakilci mazabar Vandikwa da Konshisha a jihar Benue, wacce itace ta lashe zaben fidda gwamni karkashin jam'iyyar APC ba Hembe ba.

A take kotun ta umarci Hembe da ya dawo da albshin da ya karba tun bayan rantsar dashi a shekarar 2015. Kotun ta kara da cin tarar Hembe har Naira miliyan daya.

Jaridar Premium times ta gano cewa Naira 19,058,040 ne kudaden albashi da alawus din da Hembe bai maida ba.

Ya roki kotun kolin tun a lokacin cewa zai dawo da kudin amma fa a lokacin ba su sakamakon hidimomin iyali da suka cinye kudin.

Hakazalika bai biya tarar miliyan dayan da kotun ta yankar masa ba.

Abubakar Danladi: an kwace kujerar Danladi ne rana daya da Hembe kuma an bukaci ya dawo da kudin albashin da alawus da ya karba na watanni 24 da yayi a kujerar sanata.

Danladi, sanata mai wakiltar Taraba ta arewa kafin a tsigeshi, ya karba Naira 25,532,640.

A 2018, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya zabi Danladi a matsayin mai bada shawara na musamman akan aiyuka na musamman.

Jim kadan bayan zabarsa, jaridar Premium Times ta nemi shaidar maida kudaden da Danladi ya karba daga majalisar kamar yadda kotun koli ta bukata. Har yau majalisar dattawa bata maida martani ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel