Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram 3, sun kama kayayyaki

Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram 3, sun kama kayayyaki

Dakarun rundunar Sojan Najeriya sun kaddamar da wani samame a wata mabuyar mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a kauyen Kirawa na jahar Borno, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Kaakakin rundunar Sojan kasa, Kanal Sagir Musa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a shafin hukumar Sojan kasa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda yace bayan Sojojin sun dira mafakar yan ta’addan basu yi kasa a gwiwa ba har sai da suka karkashesu.

KU KARANTA: Dahiru Bauchi ya yi karin haske game da harbe harben da aka yi a gidansa

Sagir yace wannan hari da Sojoji suka kai na daga cikin sabon tsarin da rundunar ta bullo da shi na samar da manyan sansanonin Soji a yankuna daban daban na jahar Borno, wanda ake kira a turance “Super Camp Concept of Operation.”

Sai dai Sagir yace Sojoji sun samu wannan nasara ne tare da taimakon matasa Sojojin sa kai na Civilian JTF, inda ya kara da cewa an yi musayar wuta sosai tsakanin Boko Haram da jami’an tsaron, amma Sojoji sun samu galaba, inda suka kashe 3, sauran kuma suka tsere da rauni a jikinsu.

Daga karshen artabun, Sojojin sun gudanar da bincike a mabuyar, inda suka gano kekuna guda 6, da kuma kayan abinci, a cewar Sagir, bincike ya nuna mayakan sune masu farauto ma kungiyar kayan abinci.

Daga karshe kaakaki Sagir ya tabbatar da cewa babu wani Soja da aka kashe ko ya samu rauni a dalilin harin, sa’annan ya bada tabbcin zasu cigaba da farautar yan ta’adda a duk inda suke don hana su sakat.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel