Toh fah: Ta sace yaro daga gidan marayu tare da siyar da shi

Toh fah: Ta sace yaro daga gidan marayu tare da siyar da shi

- Hukumar 'yan sanda sun kama wata mata mai suna Isaac Bose da laifin satar yaro

- Bayan sace yaron sai ta siyar da shi ga wata mata a jihar Ogun

- Tuni dai 'yan sanda sun ceto yaron tare da cafke matar da ake zargi da safarar yara

Hukumar 'yan sandan jihar Niger ta tseratar da yaron da aka sace tare da siyar da shi akan Naira 300,000.

Mata mai suna Bose Isaac ce ta siyar da yaron ga watan mata a jihar Ogun.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandar jihar, Muhammad Abubakar, ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis a garin Minna.

Tuni dai aka tura rundunar 'yan sandan yankin Kagara zuwa jihar Ogun don kamo wacce ake zargi da sayan yaron.

Northern City News sun gano cewa wacce ake zargin ta tsere daga gidanta bayan da ta ji cewa 'yan sanda na tafe.

KU KARANTA: Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fidda naira biliyan 182 don gyara da yin sabbin tituna

Abubakar yace, bincike ne ya jagoranci 'yan sandan har zuwa gidan marayu a Legas inda ake rainon yaron.

Kamar yadda yace, 'yan sanda sun koma gidan marayun a karo na biyu bayan da basu ga yaron ba a ziyararsu ta farko zuwa gidan.

An cafke Isaac bayan da mahaifin yaron, Gambo Shuaibu, na yankin cikin garin Kagara da ke karamar hukumar Rafi a jihar Minna ya kai rahoton bacewar Dansa ga 'yan sanda a ranar 24 ga watan Augustan wannan shekarar.

Wacce ake zargin ta amsa laifinta na sace yaron da kuma siyar da shi ga wata mata a jihar Ogun akan Naira 300,000.

Za a gurfanar da wacce ake zargin da safarar yara a gaban kotu don fuskantar hukunci kamar yadda Abubakar ya sanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel