An yi taho mu gama tsakanin Jirgin shugaban kasa da motar Bus

An yi taho mu gama tsakanin Jirgin shugaban kasa da motar Bus

Wata motar Bus dake dauke da yan jaridu ta yi taho mu gama da jirgin shugaban kasar Canada, Justin Trudeau, a filin sauka da tashin jirage na Whistlestop dake jahar Westernmost na kasar Canada, inji rahoton Sahara Reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya auku ne a ranar Laraba, 11 ga watan Satumba yayin da shugaba Trudeau yake gudanar da yakin neman zabe da nufin sake darewa kujerar da yake kai.

KU KARANTA: Budurwa yar Kaduna ta gamu da hukuncin bulala 80 saboda shan tabar wiwi

Wasu yan jaridu dake tare da shugaban sun bayyana cewa saukan jirgin shugaban kasar keda wuya a filin ashe akwai wata motar Bus dake tafe, basu ankara ba sai jin motar suka yi a kasan jirgin, inda ta gogi guda daga cikin fika fikan jirgin.

“Babu wanda ya samu rauni, kuma a ana nan ana duba barnar da motar ta yi ma jirgin.” Inji kaakakin jam’iyyar shugaba Trudeau, Eleanor Catenaro. Ta kara da cewa wannan akasi da aka samu ba zai shafi yakin neman zaben shugaban ba, wanda ake sa ran isarsa jahohin Kamloops da Edmonton.

A wani labari kuma, kungiyar bada agajin gaggawa ta Duniya, International Committee of Red Cross (ICRC) ta bayyana kimanin mutane 22,000 ne suka yi batan dabo a Najeriya, wanda sama ko kasa an nemesu an rasa a sakamakon matsalar tsaro ta Boko Haram.

Shugaban kungiyar, Peter Maurer ya bayyana haka yayin ziyarar kwanaki 5 daya kawo Najeriya, inda yace wannan alkalumman sune alkalumma mafi girma da aka taba samu na mutanen da suka bace a duniya.

A cewarsa, kashi 60 na mutanen da suka bace kananan yara ne, wanda hakan ke nuna dubun dubatan iyaye basu san inda yaransa suke ba ko kuma halin da suke ciki ba, da rai ko babu rai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel