Dumamar yanayi: Gwamnatin Kano za ta dauki Jami'an Gandun Daji 100

Dumamar yanayi: Gwamnatin Kano za ta dauki Jami'an Gandun Daji 100

Gwamnatin JIhar Kano za ta dauki ma'aikatan gandun daji 100 domin taimakawa wurin hana sare itatuwa a jihar da inganta tsaro.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa babban sakataren Ma'aikatar Muhalli, Alhaji Tukur Getso ne ya bayar da sanarwar yayin hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai, NAN a ranar Alhamis a Kano.

Getso ya yi bayanin cewa gwamnati ta damu sosai kan yadda ake sare itatuwa a jihar kuma tana iya kokarin ta don ganin an kawo karshen lamarin.

Ya ce akwai bukatar da dena sare itatuwa da daji barkatai saboda suna taimakawa wurin rage dumamar yanayi.

DUBA WANNAN: Kama Naziru sarkin waka: 'Yan Kannywood sun mayar da martani

Hakan yasa babban sakataren ya ce jihar "tayi nisa kan shirin ta samar da wutar lantarki daga ruwa da ke sa ran zai samar da megawatt 23 na wuta a jihar kuma hakan zai rage amfani da man fetur da kalanzir."

Ya kara da cewa idan mutane suka rage amfani da ababen da ake samu daga man fetur, hakan zai rage adadin gurbatatciyar isakar da ake samarwa a jihar.

Getso ya kuma ce rage cinkoson titi a Kano da kuma shirin da ake yi na samar da manyan bas zai taimaka sosai wurin rage gurbattacen iska a jihar.

Ya kuma ce akwai ingantaccen shiri na musamman ta jihar tayi da zai yi dai-dai da shirin gwamnatin tarayya na yaki da dumamar yanayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel