Kotu ta dakatar da majalisar dokokin Najeriya daga cusa kai cikin lamuran majalisar jihar Edo

Kotu ta dakatar da majalisar dokokin Najeriya daga cusa kai cikin lamuran majalisar jihar Edo

Wata babbar kotu wadda take zaune a Fatakwal babban birnin jihar Ribas ta dakatar da majalisar dokokin Najeriya daga yin kutse cikin al’amuran majalisar jihar Edo.

Jastis Kolawale Omotosho a cikin hukuncinsa ya ce majalisar dokokin tarayya ba ta da hurumin matsawa Gwamna Godwin Obaseki a kan lallai sai ya kaddamar da sabbin ‘yan majalisar Edo.

KU KARANTA:Yanzu-yanzu: Harin Boko Haram ya tarwatsa daruruwan mutane wasu garuruwan Borno

Majiyar Premium Times ta sanar da mu cewa kotun ta yanke wannan hukuncin ne a bisa karar da mataimakin kakakin majalisar jihar Edo tare da Henry Okhuarobo mai wakiltar gundumar Ikpoba-Okha suka shigar.

A cikin korafin da suka shigar kotun, sun nemi kotun ta dakatar da majalisar dokokin tarayya daga shiga cikin al’amuran majalisar ta su.

Omotosho ya fadi cewa, majalisar tarayya ba ta da wani iko a shari’ance wanda ya ba ta damar aikata wannan abu da take yinkurin aikatawa.

Omotosho ya ce: “Babu wata hujja dake gaban kotun wadda ke nunin cewa zaman majalisar jihar ba zai yiwu ba. An riga da an kaddamar da wasu daga cikin shuwagabannin majalisar.

“Babu sashe ko guda daya ya a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya da ya goyi bayan aikata ayyuka irin wadannan.”

Alkalin ya sake cewa, gwamnan jihar Edo shi ne shugaban majalisar zartarwa na jiharsa a don haka bai kamata a ce majalisar dokokin tarayya ke juya akalar majalisar dokokin jiharsa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel