Buhari zai tsamar da mutum miliyan 10 daga talauci a shekara 10 – Osinbajo

Buhari zai tsamar da mutum miliyan 10 daga talauci a shekara 10 – Osinbajo

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce 'yan Najeriya guda miliyan 10 za su rabu da talauci a cikin shekaru 10 masu zuwa.

The Punch ta ruwaito cewa Osinbajo ya yi wannan alkawarin ne a ranar Alhamis a fadar Abdullahi Fodio da ke Birnin Kebbi yayin da ya kai ziyarar ban girma ga Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Bashar.

Osinbajo ya ce, "Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin tsamo 'yan Najeriya miliyan 10 daga cikin talauci, muna kyautata zaton za mu cimma hakan tare da hadin kai da gwamnonin jihohi.

DUBA WANNAN: Kama Naziru sarkin waka: 'Yan Kannywood sun mayar da martani

"Mun zo Kebbi ne domin abubuwa da yawa kuma domin mu tallata shirin tallafawa kanana da matsakaitan 'yan kasuwa da kuma duba yadda aikin yi wa kasuwa garambawul ke tafiya."

A cewar Mataimakin Shugaban Kasar, an fito da tsarin tallafawa kananan da matsakaitan 'yan kasuwa ne domin rage radadin talauci a kasar.

"Muna bawa kananan 'yan kasuwa N10,000, idan sun biya sai mu kara adadin zuwa N20,000.

"Wannan shiri ne mai kyau da aka tsara domin taimakawa 'yan Najeriya masu son aiki. Ya kamata su samu tallafi daga gwamnati komin kankanta sa," inji shi.

Ya yabawa basaraken, Alhaji Muhammadu Bashar saboda hadin gwiwa da ya yi da hukumomin tsaro domin yaki da masu tayar da zaune tsaye a jihar kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai, NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel