Kotun zabe: Nasarar Buhari zai kawo karshen kazamar siyasar PDP a Najeriya – Uba Sani

Kotun zabe: Nasarar Buhari zai kawo karshen kazamar siyasar PDP a Najeriya – Uba Sani

Dan majalisa mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Malam Uba Sani, ya bayyana tabbatar da nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kotun zabe tayi a matsayin babban nasara ga kudirin mutane a fadin kasar.

Legit.ng ta rahoto cewa kotun zaben shugaban kasa da ke zama a Abuja a ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, ta kori karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta na Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, suka shigar don kalubalantar nasarar shugaba Buhari a lokacin zaben ranar 23 ga watan Fabrairu.

Yayinda yake yaba hukuncin, Sanata Uba Sani yace sake tabbatar da nasarar zaben Buhari nuni ne ga cewar an samu yancin damokradiyya a Najeriya.

Yace mutane sun daddake wasu da suka hana Najeriya ci gaba na lokaci mai tsawo.

Don haka Sanata Sani, ya taya Shugaban kasar murnar nasarar da ya samu a kotun zaben yayinda ya jinjinawa bangaren shari’a akan tsayawa da tayi wajen cika muradin mutane, inda ya bukaci yan Najeriya da su ba gwamnati da Buhari hadin kai.

KU KARANTA KUMA: Sakon taya murna da nayi wa Buhari daga zuciyana ya fito - Wike

Dan majalisan ya kuma shawarci Atiku da jam’iyyarsa da su amshi shan kaye da zuciya daya, cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya taya Buhari murna maimakon daukaka kara a kotun koli.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel