'Yan jarida sun hada gwuiwa da kungiyoyi domin bin diddigin alkawuran da El-Rufa'i ya cika a Kaduna

'Yan jarida sun hada gwuiwa da kungiyoyi domin bin diddigin alkawuran da El-Rufa'i ya cika a Kaduna

Wasu 'yan jaridu da kungiyoyi masu zaman kansu (CSOs) sun lashi takobin gudanar da binciken bin 'kwakwafi' a kan alkawuran yakin neman zabe da gwamnan jihar Kaduna ya yi da kuma cigaba da bin diddigin sabbin alkawuran da ya dauka a cikin jawabin da ya gabatar ranar rantsar da shi.

Kazalika, sun ce zasu cigaba da bin kadin dukkan alkawuran yakin neman zabe da gwamna El-Rufa'i ya dauka tare da bayyana cewa yin hakan zai sa gwamnati ta tashi tsaye haikan wajen ganin ta cika alkawuran da ta dauka.

'Yan jaridun sun bayyana hakan ne ranar Alhamis a karshen wani taro da suka yi a garin Kaduna domin tattauna wa a kan alkawuran da gwamnan ya dauka yayin yakin neman zabe a jihar.

Kamfanin dillancin kabarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa kungiyar DFID ce ta dauki nauyin gudanar da taron a Kaduna.

Daga cikin alkawuran da gwamna El-Rufa'i ya dauka akwai batun saka bukatar mutanen jihar Kaduna a farko, bayar da hutun watanni shidda ga mata ma'aikata bayan sun haihu, kaddamar da inshorar lafiya, samar da ababen more rayuwa domin inganta rayuwar jama'ar jihar Kaduna domin su kasance masu dogaro da kan su da sauran su.

DUBA WANNAN: A cigaba da bawa 'ya'yan mu abinci kyauta idan ana so su cigaba da zuwa makaranta - Musa mai 'ya'ya 14

Kazalika, El-Rufa'i ya dauki alkawarin samar da gidaje domin bawa jama'a damar mallakar muhalli na kashin kan su da kuma inganta makarantun firamare a fadin jihar.

Mahalarta taron sun yaba wa gwamnatin jihar Kaduna bisa kirkirar ma'aikatar kula da tsaron jiha da kuma kafa kwamitocin tabbatar da zaman lafiya a kananan hukumomin jihar.

Sun bayyana cewa bangaren yada labarai da kungiyoyi asu zaman kansu na da muhimmiyar rawar da za su iya taka wa wajen ganin cewa gwamnan ya cika alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel