Dalilin da yasa nafi gamsuwa da bawa mata rikon amanar kudin Najeriya - Buhari

Dalilin da yasa nafi gamsuwa da bawa mata rikon amanar kudin Najeriya - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya bayyana cewa ya na bawa mata mukamai a fanin kudi ne domin tabbatar da cewa an takaita almubuzarranci tare da janyo su a jiki domin su ma a dama da su.

Shugaba Buhari ya yi wannan jawabin ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar shugabanin mata na jam'iyyar APC daga shiyoyi da jihohi daban daban karkashin jagorancin shugaban mata Hajiya Salamatu Umaru Baiwa a fadarsa da ke Abuja.

Ya yi bayyanin cewa ya gwammace ya nada mata a fannin kudi kamar ministan kudi saboda za su iya amfani da kwarewa da gogewarsu wurin tattalin kudi domin ganin an biya bukatun 'yan Najeriya.

DUBA WANNAN: Kama Naziru sarkin waka: 'Yan Kannywood sun mayar da martani

Ya kara da cewa akwai mata kwararru da yawa a Najeriya da suka goge a fanin kudi a gida da ma kasashen ketare kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa, "Ina farin ciki domin zan iya kare kai na kan wannan batun. Shugaban APC na kasa shine shaida na. Tun hawan mu mulki, mata muke dankawa ma'aikatan kudi.

"Ko a gidaje, mata ake bawa kudi domin su adana. Ana iya amfani da wannan tsarin a matakin kasa. Hakan yasa mata na rika nada wa ministocin kudi. Haka na tsara abin.

"Ina sane da irin gudunmawar da mata suke bayar wa a kasa. Ayyuka na ya nuna cewa da gaske na keyi."

Ya kara jadada cewa gwamnatinsa ba za tayi watsi da mata da matasa ba musamman a zangon mulkinsa karo na biyu ta hanyar basu tallafi domin su fara sana'o'i da noma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel