Yanzu-yanzu: Harin Boko Haram ya tarwatsa daruruwan mutane wasu garuruwan Borno

Yanzu-yanzu: Harin Boko Haram ya tarwatsa daruruwan mutane wasu garuruwan Borno

Mun samu labarin cewa daruruwan mutane sun gudu daga muhallansu a sakamakon wani harin da mayakan Boko Haram suka kai a garuruwan Gubio da Nganzai ranar Alhamis 12 ga watan Satumba.

Wata majiya dake kusa da wurin da wannan al’amari ya auku ta sanar damu cewa da dama daga cikin masu jama’ar garin sun gudu ne a sakamakon razana da suka yi na jin sautin bindiga.

KU KARANTA:Robert Mugabe: Shuwagabannin kasashen Afirka 10 za su halarci jana’izarsa

Wannan al’amarin ya faru ne a garuruwan biyu da misalin karfe 6:30 na yammacin Alhamis haka kuma a daidai lokacin hada wannan rahoton bamu san iya adadin bannar da harin ya yi ba.

Idan baku manta ba a ranar Laraba Gwamna Umara Zulum ya ziyarci garin GajiGanna inda ya roke jama’a da cewa kada su yi gudun hijira gwamnatinsa za tayi kokarin ganin cewa ta tsare rayuka da dukiyoyinsu.

A wani labarin na daban zaku ji cewa, Shuwagabannin kasashen Afirka goma ne za su halarci jana'izar tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe.

Mai magana da yawun fadar gwamnatin kasar Zimbabwe ne ya bada wannan sanarwa. A jiya Laraba ne aka dauko gawar tsohon shugaban kasan daga kasar Singapore zuwa Zimbabwe.

Duk da wannan shirye-shiryen rahotanni sun tabbatar mana cewa har yanzu ba a cinma matsaya guda ta ranar da wurin da za a birne gawar marigayin ba, wannan kuma abu ne dake faruwa tsakanin gwamnatin Zimbabwe da iyalan Mugabe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel