Hukumar zabe mai zaman kanta za ta zabge 'yan takara saboda karancin shekaru

Hukumar zabe mai zaman kanta za ta zabge 'yan takara saboda karancin shekaru

- Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC zata zabge 'yan takarar gwamnoni na jihohin Bayelsa da Kogi

- Zata zabge 'yan takarar ne sakamakon karancin shekaru da ta gani a takardunsu

- Hukumar tace zata fidda jerin sunayen a ranar juma'a

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC zata zabge 'yan takarar gwamnonin jihohin Bayelsa da Kogi.

Hukumar ta yi alkawarin sanar da sunayen jam'iyyun siyasa da abin ya shafa.

Kamar yadda hukumar ta fada, ta duba takardun 'yan takarar da jam'iyyun siyasa ta mika kuma zata zabge wadanda ke da karancin shekaru kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanadar.

Kwamishinan hukumar na kasa, Festus Okoye, ya sanar cewa zata kammala duba takardun 'yan takarar a ranar juma'a 12 ga watan Satumba.

Okoye yace jam'iyyun siyasa 64 ne suka yi zaben fidda gwank a jihar Bayelsa inda jihar Kogi kuwa jam'iyyu 59 ne suka yi.

KU KARANTA: Gwamnati ta yi wa 'yan Najeriya da suka dawo daga Afirka ta Kudu wani kyauta ta musamman

Yace, "Zamu fitar da takardun kowanne Dan takara kuma zamu buga a allon ofisoshin mu da ke Yenagoa da Lokaja. Kamar yadda doka ta tanadar, tuni hukumar ta kiyaye zaben fidda gwani da kowacce jam'iyya tayi kuma mun fitar da sunayen wadanda suka yi nasara a shafinmu na yanar gizo."

"Daga abinda muka sani, jam'iyyun siyasa 64 ne suka yi zaben fidda gwani a Bayelsa inda jihar Kogi muka samu 59. Jam'iyyun sun kawo mana sunayen 'yan takarar da kuma takardun 'yan takarar."

"Fitar da takardun kowanne Dan takara kuwa za mu yi shi ne don mutane su gani tare da kalubalantar duk inda suke da tantama, kamar yadda doka ta tanadar. A hakan ne muka gano cewa akwai 'yan takarar da shekarunsu bai kai na neman wannan kujerar ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel