Gara na taya Buhari murna a kan na kai masa ziyara, ba zan taba ziyartarsa ba - Wike

Gara na taya Buhari murna a kan na kai masa ziyara, ba zan taba ziyartarsa ba - Wike

Gwamnan jihar Ribas, Mista Nyesom Wike, ya bayyana dalilansa da suka sa ya taya shugaban kasa, Muhammadu Buhari, murnar samun nasara a kotun sauraron korafi a kan zaben shugaban kasa.

Gwamnan ya bayyana dalilan nasa ne ranar Alhamis yayin da ya ke gabatar da jawabi domin kare kansa daga sukar da yake sha a wurin wani taro da ya halarta a Emohua.

Masu sukar gwamna Wike na ganin bai yi wa jam'iyyarsa PDP da dan takarar ta kara ba ta hanyar gaggauta taya Buhari murnar samun nasara a kotu.

A cewar gwamnan, gara ya taya Buhari a bainar jama'a a kan ya kai masa ziyara gida a sirrance cikin dare domin taya shi murna.

Ya ce ba zai zama tamkar sauran gwamnonin jam'iyyar PDP da ke zuwa taya Buhari murna tsaar dare ba.

DUBA WANNAN: Gwamonin arewa sun fara gudanar da taro domin nema wa yankinsu mafita

"Na san dukkan ku na mamakin cewa na taya shugaba Buhari murna. Gara na taya shi murna a bainar jama'a a kan na lallaba gidansa da daddare domin yin hakan.

"Gwamnonin jam'iyyar PDP da yawa na zuwa gidansa da daddare domin taya shi murna. Ban taba zuwa ba, kuma ba zan je ba," kamar yadda gwmna Wike ya bayyana a cikin wani jawabi da Simeon Nwakaudu, mai taimaka masa a bangaren yada labarai ya fitar.

"Mu ne kadai jihar da gwamnatin tarayya ta hana kudi domin biyan aiyukan da ya kamata gwamnatin tarayya ta kaddammar saboda ban je na ga Buhari da daddare ba, ba zan taba kai masa ziyara ba.

"Ba abokina bane, ba ya kokari amma duk da haka ya samu nasara a kotu. So ake na zargi kotu da rashin yin adalci?, Wike ya tambaya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel