Mun dawo da dukkan alhazan Najeriya gida - NAHCON

Mun dawo da dukkan alhazan Najeriya gida - NAHCON

Hukumar jin dadin alhazan Najeriya wato NAHCON ta kammala dawo da dukkan alhazan da suka halarci Hajjin bana a jirgin karshe mai lamba NGL 2124 Max Air.

Shugabar sashen yada labarai na hukumar, Hajiya Fatima Usara, ta bayyana hakan ne a wani jawabi da ta saki a ranar Alhamis, 12 ga watan Satumba, 2019.

Ya bayyana farin cikin shugaban hukumar, Alhaji Abdullahi Muhammad, inda ya mika godiyarsa ga Allah kan nasarar kawo karshin aikin hajjin bana.

Mun kawo muku rahoton cewa an fara jigilar maniyyatan ne a ranar 17 ga Agusta inda aka kwashi kwanai 26 ana jigilarsu kuma aka kammala cikin sahun jirgi 91.

Shugaban NAHCON ya jinjinawa masu ruwa da tsaki kan jajircewarsa, hakuri, gudunmuwa da kokarin wajen gudanar da aikin wannan shekara.

Yace: "Addu'an wannan hukuma shine Allah ya cigaba da kare ma'aikata kan wanzar da dukkan hakkokinsu."

Hakazalika ya yabawa kamfanin jiragen Max Air da Flynas kan kokarinsu wajen jigilar mahajjata da kayayyakinsu a kan lokaci.

A wani labarin kuma, Wata kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a unguwar Magajin Gari ta jihar Kaduna, ta yanke wa wata budurwa masi shekaru 19 a duniya, Zainab Abdullahi, hukuncin bulala 80 biyo bayan kama ta da laifin shan tabar wiwi a bainar al'umma.

Da yake zartar da hukuncinsa a ranar Alhamis, Alkalin kotun Malam Muhammad Shehu Adamu, ya zartar da wannan hukunci a kan Zainab bayan ta amsa laifin da ake zarginta da aikata wa na shan tabar wiwi a filin Allah.

A rahoton da jaridar The Punch ta ruwaito, Alkali Shehu ya ce bulala 80 shi ne hukuncin da shari'a tayi tanadi ga duk wanda aka akama da laifi makamancin wanda Zainab ta aikata na shaye-shayen kayan maye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel