Buhari zai kayar da Atiku ko a 'kotun duniya' ne - Oshiomhole

Buhari zai kayar da Atiku ko a 'kotun duniya' ne - Oshiomhole

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), na kasa Kwamared Adams Oshiomhole ya yi tofa albarkacin bakinsa kan hukuncin da kotun sauraron zabe shugaban kasa ta yanke.

Oshiomhole ya yabawa kotun da ta jadada nasara Shugaba Muhammadu Buhari inda ya ce Buhari zai kayar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a duk inda aka tafi.

Ya bayyana hakan ne yayin hira da ya yi da manema labarai na gidan gwamnati bayan ganawa da ya yi da shugaban kasa tare da wasu shugabanin mata na jam'iyyar APC a ranar Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

DUBA WANNAN: Kama Naziru sarkin waka: 'Yan Kannywood sun mayar da martani

Bayan nasarar da suka samu a kotun zabe, shugaban na APC ya ce baya tantama cewa Shugaba Buhari zai kayar da abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP a kotun koli kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

A cewarsa, ko da dokar kasa ta bawa Atiku ikon zuwa kotun duniya, jam'iyyar APC a shirye ta ke ta fafata da shi a kotun.

Oshiomhole ya kuma cacaki dan takarar shugaban kasar na PDP kuma ya shawarci 'yan Najeriya suyi watsi da duk wasu dabi'u na kasashen yamma da ka iya jefa Najeriya cikin matsala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel