Robert Mugabe: Shuwagabannin kasashen Afirka 10 za su halarci jana’izarsa

Robert Mugabe: Shuwagabannin kasashen Afirka 10 za su halarci jana’izarsa

-Fadar shugaban kasar Zimbabwe ta ambaci sunayen wasu shugabannin kasashen Afirka da za su halarci jana'izar Mugabe

-Kakakin gwamnatin kasar Zimbabwe ne ya bada wannan sanarwar duk da cewa ba san hakikanin ranar birne mamacin ba

Gwamnatin kasar Zimbabwe ta fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis 12 ga watan Satumba cewa shuwagabannin kasashen Afirka goma ne ake sa ran za su halarci jana’izar tsohon Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe.

A ranar Laraba 11 ga Satumba ne aka maido da gawar Mugabe zuwa kasar Zimbabwe daga Singapore kasar da a can ne Allah ya karbi rayuwarsa.

KU KARANTA:Nasarar Buhari a kotu: Manyan lauyoyi sun jinjinawa kotun zabe saboda wannan hukunci

Marigayin ya jima zaune a kasar ta Singapore inda ya kasance yana samun kulawar likitoci tun daga watan Afrilu har zuwa lokacin da Allah ya karbi rayuwarsa.

An sanya ranar Asabar 14 ga Satumba a matsayin ranar da za a birne gawar ta sa. Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, Uhuru Kenyatta na kasar Kenya da Filipe Nyusi na kasar Mozambique na cikin shuwagabannin kasar da za su halarci jana’izar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wasu tsoffin shuwagabannin kasashen Afirka bakwai za su halarci wannan jana’iza. Tsoffin shuwagabannin sun hada da; Jacob Zuma na Afirka ta Kudu, Kenneth Kaunda na Zambia da kuma Sam Nujoma na kasar Namibia.

George Charamba, kakakin Shugaban kasar Zimbabwe ne ya fitar da wannan sanarwa. Sai dai kuma har ila yau an kasa samun matsaya guda daya dangane da rana da kuma hakikanin wurin da za a birne Mugabe a tsakanin gwamnatin kasar Zimbabwe da iyalan marigayin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel