Hotuna: Yadda hukumar SON ta kwace kayayyakin bogi na miliyoyin nairori a shagunan mutane a jihar Kaduna

Hotuna: Yadda hukumar SON ta kwace kayayyakin bogi na miliyoyin nairori a shagunan mutane a jihar Kaduna

- Hukumar tantance ingancin kaya ta kasa reshen jihar Kaduna ta yi wani sumame ga 'yan kasuwan da suke sayar da kayan bogi a fadin jihar

- Hukumar ta kai sumamen nata kan 'yan kasuwan da suke cikin birnin jihar Kaduna, inda ta shiga zuwa garin Zaria daga nan ta dangana da garin Kafanchan

- Wannan fita da hukumar tayi ta samu nasarar kwato kayayyaki masu dumbin yawa a wajen 'yan kasuwa da suke sayarwa na bogi

Hukumar tantance ingantattun kaya ta Najeriya (SON) ta fara shiga lungu da sako na fadin kasar nan domin bankado da kwace kaya marasa inganci da ake sayarwa da al'umma.

Hukumar ta dauki wannan mataki ne domin ganin ta inganta rayuwar al'umma da kuma kawo cigaba ga kamfanoni masu kera kayayyaki.

Hotuna: Yadda hukumar SON ta kwace kayayyakin bogi na miliyoyin nairori a shagunan mutane a jihar Kaduna
SON Kaduna
Asali: Facebook

Da yake magana da manema labarai a jihar Kaduna, bayan sun kammala zagaye garuruwa guda uku da suka hada da cikin birnin Kaduna, Zaria da kuma Kafanchan, domin kwace kayayyakin na bogi, shugaban hukumar jihar Kaduna Mr. D.E Datti, ya bayyana cewa bayan sun samu umarni daga wajen darakta janar na kasa Mr. Osita Aboloma, wanda ya nuna bacin ranshi akan yawaitar kayayyaki na bogi a kasuwannin kasar nan, shugaban ya bayar da umarnin shiga lungu da sako na kasuwannin kasar nan domin kwace duk wani kaya da yake bashi da kyau.

Hotuna: Yadda hukumar SON ta kwace kayayyakin bogi na miliyoyin nairori a shagunan mutane a jihar Kaduna
SON Kaduna
Asali: Facebook

KU KARANTA: Tirkashi: Naga abubuwa da yawa a lahira da mutane baza su so jin labarin su ba - In ji Likitan da ya mutu ya dawo

Mr. D.E Datti ya bayyana irin nasarar da aka samu a wannan fita da suka yi, sannan kuma ya ja kunnen 'yan kasuwa da suke sayar da kayyaki marasa kyau akan cewa hukumar su baza ta saurarawa duk wanda ta samu yana sayar da kayan bogi ba.

A lokacin da shugaban yake nunawa manema labarai irin kayayyakin da suka kwace daga wajen 'yan kasuwa masu sayar da kayan marasa inganci, ya bukaci kamfanoni da 'yan kasuwa da su dinga kwatanta gaskiya a cikin al'amuransu.

Hotuna: Yadda hukumar SON ta kwace kayayyakin bogi na miliyoyin nairori a shagunan mutane a jihar Kaduna
SON Kaduna
Asali: Facebook

Bayan haka ya shawarci mutane da su dinga siyan kayan da suka tabbatar da cewa hukumar tantance ingantattun kaya ta Najeriya (SON) ta tantance su, domin hakan ne kawai zai saka su tsira da kayayyakin su.

Hotuna: Yadda hukumar SON ta kwace kayayyakin bogi na miliyoyin nairori a shagunan mutane a jihar Kaduna
SON Kaduna
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel