Nasarar Buhari a kotu: Manyan lauyoyi sun jinjinawa kotun zabe saboda wannan hukunci

Nasarar Buhari a kotu: Manyan lauyoyi sun jinjinawa kotun zabe saboda wannan hukunci

Manyan lauyoyin Najeriya (SANs) sun jinjinawa kotun sauraron korafin zaben Shugaban kasa a bisa hukuncin da ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar Shugaba Buhari a zaben 23 ga watan Fabrairu.

Lauyoyin sun ce babu wani abin da yake a boye game da shari’ar a don haka bangaren dake karar kamata yayi su kuka da kansu, saboda gaskiya ce tayi halinta.

KU KARANTA:Bamu da niyyar sanya ‘yan Najeriya cikin halin wahala – Shugaba Buhari

Wadanda suka yi magana game da wannan hukuncin sun hada da Robert Clarke, Femi Falana da Rotimi Jacobs.

Kotun sauraron korafin zaben Shugaban kasa ce tayi fatali da karar Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta PDP wacce aka shigar a ranar 18 ga watan Maris inda ta tabbatar da cewa nasarar Buhari ta inganta.

A cewar kotun, bangaren dake kara ya gagara gabatar da shaida domin kare tabbatar da gaskiyar hujjojin dake kunshe cikin korafinsu. Hakan ne ma ya sa kotun tayi watsi da karar kai tsaye.

“A don haka munyi watsi da wannan karar.” Inji Jastis Muhammad Garba. Clarke ya gamsu da hukuncin kotun zaben.

Ya ce bangaren dake karar ya gagara kawo hujjojin da za su tabbatar da cewa lallai Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben, sabanin sanarwar da hukumar zabe ta INEC ta bada.

Clarke ya kara da cewa: “Bangaren dake kara sun fadi kasa warwas. PDP na da tawagar lauyoyi menene na kawo wani daban a kan cewa ya zo yayi jawabi a game da shafin yanar gizo na wallafa sakamakon zabe.”

Bugu da kari, Femi Falana ma ya yi makamanciyar wannan magana inda ya ce, wannan hukunci bai da wata tangarda ko guda daya.

https://thenationonlineng.net/buharis-victory-sans-hail-tribunals-verdict/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel