Tanadin da muka yiwa yan Najeriya da suka dawo daga kasar Afrika ta Kudu – Abike Dabiri

Tanadin da muka yiwa yan Najeriya da suka dawo daga kasar Afrika ta Kudu – Abike Dabiri

Shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Hon Abike Dabiri-Erewa, ta bada tabbacin cewa gwamnati za ta tallafa wa yan kasar wadanda aka dawo dasu daga kasar Afrika ta Kudu sakamakon lamarin kashe kashen dake gudana.

Rukunin farko da suka dawo kasar kimanin mutane 228 188, sun bar Afrika ta kudu a ranar Laraba a jirgin Air Peace Airline bayan sun samu jinkiri na tsawon awa takwas.

Channels TV ta ruwaito cewa an hana wasu mutane tafiya akan rashin cikakkiyar takardun tafiya da yara, sannan aka kama mutane bakwai bisa zargin shiga kasar ta haramtacciyar hanya.

Misis Dabiri wacce har ila yau ta tabbatar da cewa an samu jinkirin ne sakamakon al’amuran hukumar shige da fice, ta bayyana cewa an warware lamarin kuma kashi na farko suna hanya.

A cewar ta, daga saukan su, za a ba kowannen su layin waya da kudi a ciki wanda zai dauke su watanni biyu don taimaka musu wajen sanin wani irin hali iyalensu ke ciki.

KU KARANTA KUMA: Jami’o’in Najeriya 3 kacal ne suka yi nasarar shiga jerin manyan jami’o'i 1000 a duniya (kalli sunayensu)

"Bankin tattalin arziki ma zata kasance anan domin gudanar da wasu shirin kasuwanci da wasu tallafi don fara karamin kasuwanci sannan kuma akwai wasu yan taro-kwabo na tafiya da za a basu domin mayar dasu gida sannan za mu yi shiri ga wadanda ke son kowani irin horo, su za su yankehukunci akan irin horon da suke son yi sannan bankin za ta tanadar masu shi," inji Dabiri.

Akwai sauran sunaye a jerin sunayen wadanda suka ga daman tafiya kuma muna zatton jirgi na biyu zai isa Johannesburg don diban su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel