Gwamna Zulum ya rantsar da sabbin kwamishinoni uku

Gwamna Zulum ya rantsar da sabbin kwamishinoni uku

Gwammnan Jihar Borno Farfesa Babagana Zulum a ranar Alhamis ya rantsar da wasu sabbin kwamishinoni guda uku da ya nada.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa anyi bikin nadin ne a dakin taro na kasa da kasa da ke sakatariyar Musa Usman da ke Maiduguri bayan an tanadi matakan tsaro.

Yayin rantsar da kwamishinonin, gwamnan ya bukaci su kasance masu jajircewa wurin ayyukansu musamman wurin sake gine-gine da tallafawa wadanda ifila'i ya fada musu domin su koma gidajen su.

Gwamna Zulum ya ce taken gwamnatinsa shine 'yi wa al'umma hidima'

DUBA WANNAN: Kama Naziru sarkin waka: 'Yan Kannywood sun mayar da martani

A cewarsa, an zabi sabbin kwamishinonin ne saboda cancantarsu da rikon gaskiya.

Ya kuma ce jihar Borno ce ta fi fuskantar iftila'in ta'addanci amma kuma ita ce ke da mafi karancin kudi.

Gwamnan ya bayar da umurnin yi wa tsohon ofishin da ke sakatariyar kwaskwarima bayan watsi da aka yi da shi na tsawon shekaru.

Ya ce hakan zai bashi daman gudanar da wasu ayyuka da za su kawo cigaba a aikin gwamnati.

Da ya ke jawabi a madadin sauran kwamishinonin da aka rantsar, Kaka Shehu Lawan da aka nada a ma'aikatar Shari'a ya mika godiyarsa ga gwamnan saboda nadin da ya yi musu.

Ya yi alkawarin cewa za su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da amana.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel