Gwamnati ta yi wa 'yan Najeriya da suka dawo daga Afirka ta Kudu wani kyauta ta musamman

Gwamnati ta yi wa 'yan Najeriya da suka dawo daga Afirka ta Kudu wani kyauta ta musamman

- Shugaban hukumar 'yan Najeriya mazauna kasashen ketare tace an baiwa 'yan Najeriya da suka dawo daga kasar Afirka ta kudu kyauta

- An ba kowannensu layi mai dauke da Naira 160,400 don kira, sai 9GB don amfanin yanar gizo

- An kuma sanar dasu cewa zasu iya karbar bashi daga bankin masana'ata idan suna da bukata

A ranar Alhamis ne shugaban hukumar 'yan Najeriya mazauna kasashen ketare, Abike Dabiri-Erewa, yace 'yan Najeriya da suka dawo daga kasar Afirka ta kudu an ba kowannensu sabon layin waya mai dauke da katin Naira 160,400 tare da 9GB na amfanin yanar gizo.

Zasu iya morar wannan garabasar har na tsawon watanni biyu masu zuwa.

KU KARANTA: Babu ranar bude iyakokin kasar nan, inji shugaban kwastam na kasa

Dabiri-Erewa ya sanar da hakan ne bayan saukar 'yan Najeriyar a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke jihar Legas a ranar Laraba.

Ta kara da cewa suna da damar karbar bashi daga bankin masana'atu in har suna da bukata.

Ta kara da sanarwar cewa, bayan bashin da zasu iya karba, za a basu kudi don maida su gidajensu cikin 'yan uwansu.

Tace "Akwai shirin hadin kai da zai biyo baya."

Hakazalika an baiwa kowannensu N25,000 domin sufuri zuwa jihohinsu daga jihar Legas.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta ce za ta bullo da wasu sabbin tsare-tsare na gano wadanda ke da hannu cikin kaiwa bakaken fata hare-hare a kasar domin a hukunta su.

Gwamnatin ta kuma ce za ta fittika mutanen da ba su da izinin zama ko aiki daga kasar.

Hare-haren na kiyayan bakar fata da aka yi a kasar Afirka ta Kudu ya dauki hankulan jama'a da dama inda aka rika yin Allah-wadai da harin.

Wannan dai ba shine karo na farko da irin wannan harin ke faruwa a kasar ba.

A halin yanzu dai gwamnatin Najeriya ta janye jakadatar ta daga kasar kuma ta tura tawaga na musamman domin yin binciken yadda lamarin ya kasance.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel