Bamu da niyyar sanya ‘yan Najeriya cikin halin wahala – Shugaba Buhari

Bamu da niyyar sanya ‘yan Najeriya cikin halin wahala – Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya sanar da al’ummar Najeriya cewa gwamnatinsa ba za ta yi duk wani abinda zai jefa al'ummar kasar cikin wahala ba.

A cewarsa gwamnatinsa za ta maida hankali ne wurin tsamo ‘yan Najeriya daga cikin halin damuwa da wasu ke fama da shi da talauci.

KU KARANTA:Gwamnati za ta rufe layukan waya miliyan 9 marasa rajista – Dr Pantami

Majiyar The Nation ta ruwaito cewa Shugaban kasan yayi wannan maganar ne a lokacin da yake karbar bakuncin sabbin shugabanin kungiyar kwadago ta TUC a karkashin jagorancin shugabanta Quadri Olaleye a Fadar Shugaban kasa ta Villa dake Abuja.

Shugaba Buhari ya fadi a cikin wani zancen da babban mai taimaka masa a kan lamuran yada labarai na musamman Mallam Garba Shehu ya fitar cewa: “Magana a kan farashin man fetur na aminta da batunku na cewa akwai bukatar mu kawar da cin-hanci a fannin.

“Ina so in tabbatar maku da cewa a matsayinmu na gwamnati bamu da wata niyyar jefa al’ummarmu cikin halin matsi ko kuma wahala.”

Bugu da kari, Shugaban ya ce har yanzu gwamnati na nan a kan bakarta game da kaddamar da biyan sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar.

A cewarsa taron FEC na ranar Laraba 11 ga Satumba ya tattauna a kan matsalolin da suka shafi tsarin yadda za soma biyan sabon mafi karancin albashin da kuma wasu ayyuka masu kama da shi.

Buhari ya kara da cewa, a wa’adin farko gwamnatinsa ta mayar da hankali ne wurin sake farfado da martabar Najeriya ta hanyar habbaka tattalin arziki da kuma sauwakewa jama’a hanyoyin gudanar da kasuwanci. Duk da cewa ayyukan su yi alfanu, amma ya kara bada tabbacin cewa akwai sauran romon dake tafe a cikin wannan wa’adin na biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel