Buhari da shugabanin mata na jam'iyyar APC suna ganawa a Abuja

Buhari da shugabanin mata na jam'iyyar APC suna ganawa a Abuja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya shiga taro da shugabanin mata na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a fadarsa ta Aso Rock da ke Abuja

The Nation ta ruwaito cewa wadanda suka samu halartan taron sun hada da shugabanin mata na jam'iyyar a matakin kasa, shiyya, jihohi da na babban birnin tarayya, Abuja.

Sun fara taron ne misalin karfe 3 na rana a fadar shugaban kasar da ke birnin tarayya.

Anyi imanin cewa matan sun taka muhimmiyar rawa yayin zaben Fabrairun 2019 da ta bawa shugaban kasa damar zarcewa karo na biyu.

DUBA WANNAN: Kama Naziru sarkin waka: 'Yan Kannywood sun mayar da martani

Ba a fito daga taron ba a lokacin rubuta wannan rahoton.

A baya, Legit.ng ta kawo muku cewa shugaban kasar ya gana da shugabanin kungiyar 'yan kasuwa na Najeriya wato TUC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel