Gwamnati za ta rufe layukan waya miliyan 9 marasa rajista – Dr Pantami

Gwamnati za ta rufe layukan waya miliyan 9 marasa rajista – Dr Pantami

Ministan sadarwa na Najeriya, Dr Isa Ali Pantami ya ce a halin da ake ciki yanzu akwai kimanin layukan wayar salula miliyan 9 da ake amfani da su a Najeriya ba tare da rajista ba.

Isa Ali Pantami ya ba wa hukumar kula da ma’aikatun sadarwa ta kasa wato NCC umarnin cewa su gaggauta rufe layukan har sai masu layin sun bayyana kawunansu.

KU KARANTA:Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fidda naira biliyan 182 don gyara da yin sabbin tituna

A wani labarin mai kama da wannan zaku ji cewa, majalisar zartarwar Najeriya ta aminta da fidda naira biliyan 182 domin gyara da kuma yin sabbin tituna.

A ranar Laraba, 11 ga watan Satumba ne majalisar ta aminta da fitar da wannan kudin a lokacin taron da majalisar na ranar da ake yi a ko wane mako.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya jagoranci zaman da kansa wanda aka gudanar a fadar Shugaban kasa ta Villa dake Abuja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel