Matsalar tsaro: Red Cross ta bayyana yan Najeria 22,000 da ba’a san inda suke ba

Matsalar tsaro: Red Cross ta bayyana yan Najeria 22,000 da ba’a san inda suke ba

Kungiyar bada agajin gaggawa ta Duniya, International Committee of Red Cross (ICRC) ta bayyana kimanin mutane 22,000 ne suka yi batan dabo a Najeriya, wanda sama ko kasa an nemesu an rasa a sakamakon matsalar tsaro ta Boko Haram.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito shugaban kungiyar, Peter Maurer ya bayyana haka yayin ziyarar kwanaki 5 daya kawo Najeriya, inda yace wannan alkalumman sune alkalumma mafi girma da aka taba samu na mutanen da suka bace a duniya.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Kotu ta bayar da belin Naziru Sarkin waka a Kano

A cewarsa, kashi 60 na mutanen da suka bace kananan yara ne, wanda hakan ke nuna dubun dubatan iyaye basu san inda yaransa suke ba ko kuma halin da suke ciki ba, da rai ko babu rai.

“Duk wasu iyaye na kirki tashin hankalinsu shi ne rashin sanin inda y’ay’ansu suke, wannan shine halin da iyaye suke ciki a Najeriya, an barsu kullum suna cikin kokarin neman yayansu, amma mun samu da kyar mun gano mutane 367 daga shekarar 2013 zuwa yanzu.” Inji shi.

Wata mata da majiyarmu ta zanta da ita mai suna Falmata Amodu wanda danta ya bace tun a shekarar 2013 yana dan shekara 10 a lokacin ta bayyana cewa:

“Damuwata shine ban san halin da yake ciki ba, yana nan da rai ko kuwa, a duk lokacin da na yi ma kannensa girki sai na tuna da shi. A shekaru uku da muka yi a Maiduguri kullum mijina yana cikin tashin hankali, har mafarke mafarkensa yake yi, idan yana barci zaka ji yana kiran sunansa “Alkali, Alkali, Alkali”

Daga karshe Maurer ya kara da cewa iyalai ne wadanda suka fi tabuwa a sakamakon rikicin Boko Haram da aka kwashe tsawon shekara 10 ana bugawa, an raba masoyi da masoyi, an kashe yara kanana a harin bamabamai, an lalata asibitoci da gidaje.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel