A cigaba da bawa 'ya'yan mu abinci kyauta idan ana so su cigaba da zuwa makaranta - Musa mai 'ya'ya 14

A cigaba da bawa 'ya'yan mu abinci kyauta idan ana so su cigaba da zuwa makaranta - Musa mai 'ya'ya 14

Musa Malala, wani uba mai 'ya'ya 14, ya roki gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, da ya kwaikwayi tsarin gwamnatin gwamnatin tararra na ciyar da yara a makaratun firamare domin magance matsalar yawaitar yaran da basa zuwa makaranta a jihar Gombe.

Malala ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wata tattauna wa da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a garin Dukku da ke jihar Gombe. Ya ce kaddamar da shirin zai bawa iyaye kwarin gwuiwa wajen saka 'ya'yansu a makarantun boko.

A cewarsa, tun da aka daina bayar da abinci kyauta a makarantun firamare dalibai da dama suka daina zuwa makaranta kuma iyayensu basu damu ba, saboda shirin ciyarwar na taimakon iyayen yara sosai.

"Ina da mata biyu da 'ya'ya 14, kuma maganar gaskiya shine ina matukar shan wuya wajen kokarin ganin yara na sun je makaranta.

DUBA WANNAN: Gwamonin arewa sun fara gudanar da taro domin nema wa yankinsu mafita

"Yara da dama sun daina zuwa makaranta saboda an daina bayar da abinci kyauta, kuma dalilin da suke bayar wa shine; 'babu abinci, babu makaranta' wato idan ba za a ci gaba da bawa yaransu abinci ba, yaransu ba za su je makaranta ba.

"Ina kira ga gwamnan mu, Inuwa Yahaya, da ya cigaba da wannan tsari na ciyar wa kayuta domin bawa yara karfin gwyuiwar cigaba da zuwa makaranta.

"Cigaba da shirin zai taimaka sosai wajen komawar yara da yawa makaranta," a cewar Malala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel