A kan N15,000 mu ke sayen gwanjon kayan sojoji - Masu garkuwa da mutane

A kan N15,000 mu ke sayen gwanjon kayan sojoji - Masu garkuwa da mutane

Wasu mambobin kungiyar masu garkuwa da mutane da aka kama wadanda ke da hannu a garkuwa da daliban jami’ar Ahmadu Bello, sun bayyana cewa sun siya kayan sojojin da suka yi amfani da shi wajen gudanar da aikin fashi akan N15,000 daga hannun masu siyar da kayan gwanjo.

Yan fashin wadanda suka kasance cikin masu laifi 58 da rundunar yan sanda ta gurfanar a Abuja a ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, sun kuma dauki alhakin sace dan majalisar wakilai daga jihar Sokoto.

Har ila yau sun karbi bakin cewa an biya su naira miliyan 5.5 a matsayin kudin fansa don sake daliban da suka sace yayin da suke tafiya daga Abuja zuwa Kaduna.

Hakazalika an gurfanar da wata kungiyar yan fashi da ke da nasaba da sace wasu yan kasar Turkiyya a jihar Kwara.

Wani dan kungiyar, Kabiru Abdullahi ya bayyana cewa “sauran sun yi mini karyan cewa an biya su naira miliyan shida, alhalin naira miliyan 10 suka karba a matsayin kudin fansa. Naira 450,000 ne kacal abunda suka bani, amman yan sanda sun kwace kudaden bayan an kama mu.”

Kakakin rundunar yan sanda, DCP Frank Mba yace takwas daga cikin masu laifin suna da hannu a garkuwa da dan majalisar Kaduna, Suleiman Dabo, inda suka kara da cewa sun karbi bakin amsan naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa kafin sake wadanda suka sace.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Barayi sun kashe wani babban dan kasuwa, sun tsere da N590,000

Daga cikin kayan da aka kwato akwai bindigogin AK-47 guda 18, alburusai 1,233, bindigogi kanana da manya da kuma motocin sata.

Mba yace za a gurfanar da masu laifin bayan an kammala bincike.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel