Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin gina layin dogon Kano zuwa Ibadan a kudi $5.3bn

Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin gina layin dogon Kano zuwa Ibadan a kudi $5.3bn

Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ya bada daman amfani da kudi dala biyan biyar da rabi wajen ginin layin dogon garin Ibadan zuwa birnin Kano.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 12 ga watan Satumba, a taron masu ruwa da tsaki a sashen arzikin ruwa.

Yace: "A jiyan nan, an bada damar gina layin dogon Ibadan zuwa Kano na kudi $5.3bn. Hakazalika mun nemi a bamu kudi domin gina layin dogon Port Harcourt zuwa Warri."

A farkon makon nan, mun kawo muku rahoton cewa shirye-shirye sun yi nisa don fara sayar da tikitin shiga jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja a shafukan yanar gizo don kauce ma badakalar da ake samu a tashoshin jirgin, wanda hakan ke janyo rikici tsakanin matafiya da jami’an hukumar.

KU KARANTA: Sama da mutane 800 ne suka nuna bukatar takarar zaben da za a yi a jihar Kebbi

Jaridar Leadership ta ruiwato hukumar da hakkin tsara cinikin yanar gizo a Najeriya ya rataya a wuyarta, watau, Infrastructure Concession Regulatory Commission, ICRC, ce ta bayyana haka yayin ta bakin shugabanta, Chidi Izuwah yayin da yake mika takardun kasuwancin ga ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana cewa: “Ka yi alkawarin samar da mafita ga yamutsin da ake samu a tashoshin jiragen kasa, don haka a yau muka kawo maka cikakken takardar kasuwancin sayen tikiti ta yanar gizo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel