Shari’ar zaben Sanata: Kai ya rabu game da nasarar ministan Buhari a kotu

Shari’ar zaben Sanata: Kai ya rabu game da nasarar ministan Buhari a kotu

An samu rabuwar kawuna da rashin magana da murya daya tsakanin Alkalan dake sauraron korafin da tsohon gwamnan jahar Akwa Ibom Sanata Godswill Akpabio ya shigar a gaban kotun sauraron kararrakin zaben Sanatan mazabar Akwai ta Arewa maso yamma.

Shi dai Sanata Akpabio dan jam’iyyar APC ne, wanda a yanzu haka shi ne ministan dake kula da ma’aikatar Neja Delta ya shigar da karar abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Sanata Chris Ekpenyong wanda INEC ta sanar dashi a matsayin wanda ya lashe zaben 2019, inda yake kalubalantar nasarar Chris.

KU KARANTA: Daliban Kaduna za su daina amfani da takarda da biro wajen zana jarabawa

Amma a karshen zaman sauraron karar, shugaban kotun, mai Sharia W.O Akanbi tare da mai sharia Ebetu sun tabbatar da halascin zaben Chris tare da yin watsi da koken Sanata Akpabio, sai dai gudan Alkalin, mai sharia Sheriff Hafizu ya saba ma abokan aikinsa, inda yace tabbas an tauye ma Akpabio hakinsa ta hanyar soke kuri’unsa da dama, wanda da ba don haka ba da ya lashe zaben.

Da yake yanke nasa hukuncin a ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, Hafizu ya bayyana cewa hujjoji sun nuna kwacen nasara aka yi ma Akpabio a ranar zaben 23 ga watan Feburairu, kuma shi ne ya lashe zaben don haka shi ya kamata INEC ta sanar a matsayin wanda ya samu nasara ba Chris ba.

Hafizu ya jingina ra’ayinsa ne ga bayanin wani shaida da aka gabatarma kotun, Dakta William wnada ya tabbatar ma kotun cewa sun sauya adadin kuri’un da Akpabio ya samu a ofishin INEC, kuma shugaban INEC na jahar, Mike Igini ne ya umarcesu su yi hakan, inda yace haka bai halasta ba.

Haka zalika Hafizu ya caccaki INEC game da soke kuri’un APC 61, 329 a karamar hukumar Essien Udim, inda ta PDP ta samu kuri’u 9,050. Amma da yake shi kadai ne ke da wannan fahimta cikin Alkalai 3, sauran biyun sun rinjaye shi, dole kotun ta yi watsi da karar Akpabio.

Daga karshe lauyan Akpabio, Adekunle Oyesanya ya jinjina ma Hafizu bisa jajircewar daya nuna tare da rashin tsoro wajen bayyana fahimtarsa karara ba tare da jin shayin kowa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel