Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Barayi sun kashe wani babban dan kasuwa, sun tsere da N590,000

Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Barayi sun kashe wani babban dan kasuwa, sun tsere da N590,000

Rundunar yan sandan jihar Osun, a ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, tace ta kaddamar da farautar makasan wani dan kasuwa, Lukman Owoade, a yankin Oke Ayepe da ke Osogbo.

Majiyoyi a yankin sun fada ma majiyarmu ta Punch cewa marigayin na kasuwancia yankin Oke Baale da ke babban birnin jihar.

An tattaro cewa marigayi Owoade ya tafi wani taro na wata kungiya da yake ciki, kuma sannan kasancewar zubi ya kai kansa na kwasar kudin da suka tarawa, dole ya tsaya har karshen taron.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa jim kadan bayan Owoade ya karbi kudin kimanin N590,000, sai wasu barayi suka mamaye wajen, suka harbe shi sannan suka sassara shi.

Wani shaida, wanda ya nemi a boye sunans, ya bayyana cewa bayan fama da maharan na dan lokaci sai marigayin ya yanke jiki ya fadi.

Da aka tuntube shi, kwamishinan yansandan jihar, Abiodun Ige, yace, “a ranar Asabar da misalin karfe 9:30 na rana, wani Aranse Sikiru ya kai rahton cewa yayinda shi da mambobin kungiyarsa ke taro a yankin Oke Ayepe da ke Osogbo, wasu yan bindiga sun kai mamaya wajen taron sannan suka harbi marigayin.

“Mai karan ya kara da cewa maharan sun karbi N590,000 daga hannun Owoade a taron.

KU KARANTA KUMA: Kuma dai: APC ta sake rasa kujerun majalisar tarayya guda 2 a kotun zabe

“Jami’anmu sun ziyarci wajen sannan aka dauke mutumin zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Ladoke Akintola da ke Osogbo inda aka tabatar da mutuwarsa.”

Ige, wanda yace rundunar na kokarin kamo masu laifin, ya bayar da tabbacin cewa za a kama su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel