'Yan ta'adda masu nasaba da IS sun kashe sojojin Najeriya 9, 27 sun bata

'Yan ta'adda masu nasaba da IS sun kashe sojojin Najeriya 9, 27 sun bata

A kalla sojojin Najeriya 9 ne suka mutu yayin da wasu 27 suka bata bayan wasu 'yan ta'adda masu nasaba da kungiyar IS sun kai musu wani harin kwanton bauna a yankin arewa maso gabas, kamar yadda majiyar rundunar soji ta sanar da kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa, AFP.

'Yan ta'addar sun kai wa tawagar sojojin hari da manyan bindigu da gurneti mai nisan zango yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Gudumbali da ke jihar Borno a ranar Litinin, a cewar majiyar.

Kungiyar ISWAP mai wakiltar kungiyar IS a kasashen Afrika ta yamma ta ce ita ce ta kai hari kan rundunar sojin tare da bayyana cewa ta kashe dakarun soji da kuma raunata wasu da dama.

Wani jami'in soji ya fada wa AFP da yammacin ranar Laraba cewa: "ya zuwa yanzu an samu gawar sojoji 9. Ba a san inda dakarun soji 27 suke ba, ba a ga gawarsu ba.

Wani jami'in soji ya tabbatar da kai harin da kisan dakarun sojin tare da bayyana cewa; "ana cigaba da neman sauran sojojin."

Rundunar sojin na kan hanyarsu ta zuwa Gudumbali ne domin taimaka wa dakarun soji daga jamhuriyar Nijar da Chad domin kwato garin daga hannun 'yan ta'adda, a cewar majiyar.

DUBA WANNAN: Daliba ta kashe kan ta bayan jinin al'ada ya bata mata kayan makaranta saboda rashin 'kunzugu'

Kungiyar ISWAP ta yi ikirarin cewa ta lalata motocin yakin rundunar soji tare da kwace wasu motocin yakin yayin harin.

A ranar Laraba ne rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta fitar da sanarwar cewa ta lalata wasu motocin yaki na kungiyar ISWAP a gari Garunda mai makwabtaka da Gudumbali.

Tun a cikin shekarar da ta gabata kungiyar ISWAP ke kai hare-hare a kan sansanin sojoji tare da kashe dakarun soji masu yawa.

Wani tsagi na kungiyar Boko Haram ne ya rikide zuwa kungiyar ISWAP mai kai hare-hare a kasashen gefen tekun Chadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel