Kuma dai: APC ta sake rasa kujerun majalisar tarayya guda 2 a kotun zabe

Kuma dai: APC ta sake rasa kujerun majalisar tarayya guda 2 a kotun zabe

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Akwa Ibom ta sake rasa wasu kujerunta na tarayya guda biyu yayinda kotun zabe da ke zama a Uyo a ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, ta yanke hukunci inda ta ba jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) nasara.

Kujerar da suka rasa a hannun PDP sune na mazabun Abak/Etim Ekpo/Ika da Eket wanda shugabar kotun zaben, Justis Jennifer Ijohor ta kaddamar da Aniekan Umanah da Pat Ifon a matsayin wadanda suka lashe zaben.

Dan takarar APC a mazabar Abak/Etim Ekpo/Ika, Emmanuel Ekon ya kalubalanci nasarar Umanah na PDP yayinda Kufre Akpabio na APC ma ya kalubalanci kaddamar da Pat Ifon na PDP a matsayin wanda ya lashen Eket.

A bukatar da suka gabatar daban-daban, masu karar sun roki kotun da ta soke zabukan kan hujjar cewa ba a bi gudanarwar dokar zabe ba, sannan ta soke satifiket din da aka baiwa wadanda ake kara a matsayin wadanda suka lashe zaben ranar 23 ga watan Fabrairu.

Kotun ta fara yanke hukunci akan wata bukata da masu karar suka nema na hana wadanda ake kara kare shari’an kan cewa wadanda akekaran sun zame daga tsarin.

KU KARANTA KUMA: Ranar da ta zamo mafi muni gareni a matsayin Sarkin Kano - Sanusi

Sai dai kuma kotu ta yi watsi da bukatar masu karar sannan ta bayyana cewa wadanda ake kara na da dammar kare shari’an cewa sun yi hakan bisa ga ka’idar dokar.

Kotun tayi nazari akan hujjojin da dukkain shaidun masu karar suka gabatar inda ta bayyana cewa basu isa hujjar cewa ba a bi ka’idar zabe ba wanda har zai sa kotu ta goyi da bayan masu kara ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel