Sahihan dalilan da suka sa tsohon shugaban kasa Jonathan ya yi wa Alamieyeseigha afuwa

Sahihan dalilan da suka sa tsohon shugaban kasa Jonathan ya yi wa Alamieyeseigha afuwa

- Tsohon alkalin alkalai kuma ministan shari'a ya bayyana dalilan da suka sa aka yi wa marigayi Alamieyeseigha afuwa

- Hasalima, ba da gwamnatin Goodluck Jonathan aka fara shirin Yafiyar ba

- Babu bata lokaci kuma marigayi tsohon gwamnan ya cika alkawarin yarjejeniyar da aka yi da shi

Tsohon alkalin alkalai kuma ministan shari'a, Mohammed Adoke, ya bada sahihan dalilan da suka sa gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan daga ma marigayin Diepreye Alamieyeseigha kafa duk da kamasa dumu-dumu da aka yi da laifin rashawa.

Adoke ya bada bayanan rawar da ya taka a lokacin wadda ta jawo cece-kuce din mutane.

Goodluck Jonathan ya yafewa Alamieyeseigha ne a watan Maris na shekarar 2013. An yafe musu ne tare da wasu masu laifi har da tsohon shugaban bankin arewa, Shettima Bulama.

Adoke ya ce, gafarar da aka yi wa Alamieyeseigha ba wai hukuncin Jonathan ba ne. Yar'adua ne ya fara maganar dalilin samunsa da marigayi tsohon gwamnan yayi.

KU KARANTA: Babu ranar bude iyakokin kasar nan, inji shugaban kwastam na kasa

Yace, tsohon shugaba Yar'adu yayi yunkurin yafewa marigayi tsohon gwamnan amma kash, sai ciwo ya kwantar da shi wanda ashe na ajali ne.

"Lokacin da Jonathan ya zama shugaban kasa, Alamieyeseigha ya kara mika rokon yafiyarsa." Inji Adoke.

"Saboda muhimmancin alkawarin yafiyar, Alamieyeseigha ya taimaka wajen kawo zaman lafiya a yankin Niger Delta. An rage watanda da satar man fetur sosan gaske. A don haka ne aka samu bunkasar samuwar man fetur a yankin Niger Delta."

"A lokacin na tunatar da gwamnati cewa laifin Alamieyeseigha rashawa ce kuma a lokacin tunkarar zabe ake yi. Hakan kuwa zai zama barazana babba ga gwamnatin."

"Jonathan ya aminta da zancena kuma ya sanar da Alamieyeseigha dalilin da zai hana a gafarta masa," inji Adoke.

"A watan Maris 2013, lokacin da aka sake tado zancen yafiyar, sai aka tuna da yarjejeniyar da ke tsakanin Yar'adua da Alamieyeseigha, kuma tabbas tsohon gwamnan ya taka rawar gani wajen cika alkawarinsa."

A don haka ne aka yafewa marigayi tsohon gwamnan laifukansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel