Kudin tsaro: Shugaban Gwamnoni ya yi wa Hafsun Soji raddi a Abuja

Kudin tsaro: Shugaban Gwamnoni ya yi wa Hafsun Soji raddi a Abuja

A Ranar Laraba, 11 ga Watan Satumban nan ne aka samu wata takkadama tsakanin Gwamna Dr Kayode Fayemi da shugaban sojojin kasa watau Laftanan Janar Tukur Buratai kan kudin tsaro.

Shugaban hafsun Sojin na Najeriya ya fito yana cewa kudin da ake warewa gwamnonin jihohi da sunan kason tsaro ba ya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya don haka ya ce kudin ya sabawa dokar kasa.

Janar Tukur Yusuf Buratai ya nemi a rika bincike tare da bin diddikin yadda gwamnoni ke kashe wannan makudan kudi wanda a ganinsa yana cikin abin da yake karo jawo tabarbarewar tsaro a kasar nan

Gwamnan Ekiti wanda shi ne shugaban gwamnoni mai jagorantar kungiyar NGF, ya maida martani a Hedikwatar hukumar ICPC mai yaki da masu satar kudin kasa da ke babban birnin Abuja a jiya.

Kayode Fayemi ya nuna cewa soke kason da aka saba ba gwamnoni domin magance matsalar tsaro zai kawo matsaloli a jihohi. Dr. Fayemi ya ce ba hakan ne zai yi maganin satar kudin gwamnati ba.

KU KARANTA: Jirgin farko ya iso Najeriya bayan barkewar rigimar Afrika ta Kudu

Gwamnan ya ke cewa muddin aka daina ba jihohi wannan makudan kudi, za a samu dakilewar cigaba da kuma karuwar rashin tsaro tare da jinkiri daga gwamnoni wajen maganin matsaloli.

Dr. Fayemi yake cewa daina ba gwamnonin kasar wannan kudi kamar yadda wasu ke kira, zai sake jefa jihohi ne cikin matsala tare da nuna cewa an dade ana amfani da wannan tsari.

Shugaban gwamnonin ya kawo hujjoji daga wani littafi da Cif Jerome Udoji ya taba rubutawa a jawabin na sa inda ya tabbatarwa Duniya cewa wannan kudi su na cikin doka da tsarin mulki.

Kamar yadda mu ka samu labari, gwamnan kasar ya ce ko da an canzawa kudin suna, amma tun kafin zuwan sojoji mulki ake warewa jihohin Najeriya makudan kudi domin sha’anin tsaro.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel