EFCC ta kama madamfaran yanar gizo 13 a Abuja da Ilorin

EFCC ta kama madamfaran yanar gizo 13 a Abuja da Ilorin

Jami'an hukumar yaki da rashawa ta Najeriya EFCC, ta samu nasarar cafke wasu madamfaran yanar gizo 13 a birnin Ilorin da kuma Abuja.

Hukumar mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati, ta samu nasarar cafke ababen zargin takwas a yayin wani simame da jami'anta suka kai wani gida mai lamba 16 a Isaaya Shukari Crescent da ke unguwar Gwarimpa da kuma C15 da A27 a David Estate da ke unguwar Life Camp a birnin Abuja.

Mazambatan takwas da suka shiga hannu a ranar 9 ga watan Satumba cikin birnin Abuja sun hadar da; Chiyiri Izuchi, Nurala Eze Kamchi, Amuka Shadrack, Nwegbediegwu Chekwubechukwu J, Chigbo Eze, Franklin Okafor, Ezeagwu Olisaemeka da kuma Nnamani Chukwudera.

Sauran ababen da hukumar EFCC ta samu a hannun masu laifin sun hadar da wayoyin salula dama, na'aurorin kwamfuta mai tafi da gidanka, fasfo, motoci na alfarma samfuri daban-daban da suka hadar da Toyota Corolla, Toyota Avalon, Lexus, Mercedes C350, C280, GLA 280 da kuma Acura.

KARANTA KUMA: An yi wa wata yarinya bulala 80 da laifin shan tabar wiwi a jihar Kaduna

Hukumar EFCC a reshenta da ke birnin Ilorin na jihar Kwara, ta cafke Stephen Odanye, Abolarin Kayode, Babatunde Muhammad, Adepoju Tomiwa da kuma Akinbamidele Femi, wadanda ake zargi da aikata laifuka na zamba ta yanar gizo.

A yayin da hukumar EFCC ta dukufa wajen gudanar da bincike, ta ce za ta gurfanar da ababen zargin a gaban Kuliya inda kowannensu zai fuskanci hukunci kwatankwancin laifin da ya aikata.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel