Bamu taba kawo wa Buhari zai yi nasara ba a kotun sauraron karar zabe - Bitrus Porgu

Bamu taba kawo wa Buhari zai yi nasara ba a kotun sauraron karar zabe - Bitrus Porgu

Wata kungiya ta Middle Belt Forum, MBF, wadda ta fito daga yankin tsakiyar Najeriya, ta ce kungiyar lauyoyin da ta jagorancin zaman kotun sauraron karar zaben shugaban kasa, ta gaza a kan hukuncin da zartar dangane da gabatar da shaidar takardun karatu na bogi da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.

Shugaban kungiyar MBF na kasa, Dakta Bitrus Porgu, shi ne ya bayyana hakan a yayin mayar da martani dangane da hukuncin da kotun daukaka karar zaben shugaban kasa ta zartar, lamarin da ya ce yanke hukuncin bai kammala ba har sai kotun koli ta zartar da na ta hukuncin dangane da rantsuwa kan karya da shugaba Buhari yayi.

Dr Porgu a yayin zantawa da manema labarai na jaridar Vanguard ta hanyar wayar tarho, ya ce su na sa ran dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda suka goyo wa baya a yayin zaben kasa, zai daukaka kara kan hukuncin da kotun kararrakin zaben ta zartar.

A ranar Larabar da ta gabata ne kotun da ke sauraron korafin zaben shugaban kasa da aka gudanar a bana, ta yanke hukunci inda ta yi watsi da karar Atiku Abubakar, ta kuma tabbatar da nasarar jam'iyyar APC da dan takararta wato shugaba Buhari.

KARANTA KUMA: 'Yar Najeriya ta zama 'yar majalisa a kasar Canada

Shugaban kasa Buhari a yayin bayyana farin cikinsa dangane da hukuncin da kotun ta zartar, ya ce wannan nasara ce ga ‘yan Najeriya wadanda suka kada masa kuri'u a yayin babban zaben kasa.

Duk da cewar shakku na rashin samun nasara bai taba riskarsa ba, shugaban kasar ya ce ya sadaukar da wannan nasara da ya samu ga Ubangiji da kuma sauran ‘yan Najeriya inda kuma ya yabawa Alkalai da su ka yanke hukunci ba tare da tsoro ko son rai ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel