Aiki daya tak jam'iyyar PDP ke tunkaho da shi a Kaduna - El-Rufai

Aiki daya tak jam'iyyar PDP ke tunkaho da shi a Kaduna - El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya ce jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ba za ta sake yin wani tasiri ba a jihar kuma aiki guda daya kacal suka yi a jihar da za a iya nuna wa.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke jawabi ga magoya bayan jam'iyyar ta APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murna kan nasarar da ya samu a kotun karrarakin zabe na jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

El-Rufai ya ce jam'iyyar ta PDP ta lalata jihar na tsawon shekaru 16 da su kayi suna mulki tare da almubazarranci da kudin talakawa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Da izinin Allah, PDP ba za ta sake tasiri a jihar ba. Ba za muyi magana da yawa ba saboda idan Allah ya baka mulki, abinda ya dace kayi shine ka mayar da hankali kan aikin ka saboda Allah ya sawake maka ayyukan ka.

"Ba mu magana kan rashin adalcin da su kayi, ba mu magana kan kudin talakawa da suka banattar wurin gida gidaje kuma ba su gyra ruwa ba. Ba su samar da tittuna da kasuwanni ba.

DUBA WANNAN: An kama 'yan kungiyar Oro guda tara da suka kai wa musulmi hari a Ogun

"Kawai sun lalata garin da ya kamata ace sun gyra ne, sun raba wa abokansu filaye domin gina shaguna. Dukkan kudaden da aka basu na tsawon shekaru 16, ba za su iya nuna muku wani aiki da su kayi ba illa babban titin Kawo," inji shi.

El-Rufai ya kuma ce lokacin da ya zama gwamnan jihar, an bukaci wasu da su kayi aiki karkashin gwamnatin PDP su dawo da kudaden da suka wawushe.

"Ba zan tsine musu ba saboda an bukaci in dena tsine wa mutane," a cewarsa.

A martanin da tayi ta bakin sakataren hulda da jama'a na jam'iyyar Abraham Alberah Catoh, PDP ta karyata abinda gwamnan ya fadi. Ta ce an yi ayyuka da dama cikin shekaru 16 ga jam'iyyar ta mulki jihar.

Ya lissafa ginin sabon gidan gwamnatin jihar, gyara da fadada shataletaken Lugard Hall da titin Kawo, gina makarantu fiye da 200, gina cibiyoyin kulawa da lafiya guda 150, aikin ruwan Zaria, gina jami'ar jihar Kaduna (KASU), daukaka darajar asibitocin karkara 23 zuwa manyan asibitoci, gina titi mai tsawon kilomita 5,000 da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel