Ranar da ta zamo mafi muni gareni a matsayin Sarkin Kano - Sanusi

Ranar da ta zamo mafi muni gareni a matsayin Sarkin Kano - Sanusi

Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi Lamido yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara nuna jajircewa a yaki da take yi da yunwa a fadin kasar. Ya kuma yi bayanin wani yanayi da ya taba riskar kansa, inda ya bayyana hakan a matsayin rana mafi muni a gare shi a matsayin sarkin Kano.

Akan yunwa, yace gwamnati tana iya magance lamarin ta hanyar kafa hukuma mai zaman kanta sannan kuma a dunga tura mata isasshen kudi.

Basaraken ya fadi haka ne a Abuja a ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, a taron kara ma juna sani wanda kungiyar Nutrition Society of Nigeria (NSN) ta shirya.

Sanusi, wanda har ila yau shine shugaban majalisan amintattu na NSN yace abun bacin rai ne ganin yunwa na kashe yara da mata da yawa a kasar.

Yace ya kamata gwamnati ta nuna kulawa ba kama hannun yaro a yakinta da yunwa.

Yayi korafin cewa jihar shi (Kano) ta kasance kan gaba a masu fama da yunwa a kasar da kaso 58% na masu fana da yunwa.

Ranar bakin cikin

Da yake bayanin ranar bakin ciki gare shi a matsayin sarki, Sanusi yace bai kai shekara guda bayan ya hau mulki.

Yace wata mata ta zo neman tallafin kudi domin ta siyawa yaronta magani amma bata kai gare shi ba yaron ya mutu a hannunta.

"A wannan rana ina zaune akan kujerar sarauta, sai naji ihu daga baya sannan nace su je su duba, Da suka dawo sai aka fada mun wata mata ce ke jira domin neman taimako daga wajen sarki don siyawa danta magani sannan yayinda take jira, yaron ya mutu a hannunta.

"Nawa take nema, kasa da naira 3,000. idan da kun san abunda yake nufi rayuwa akan kasa da dala guda a kullun, haka yake ga macen da ke kallon danta na mutuwa a gaban idota saboda ba za ta iya siyan maganin N3,000 ba. wannan shine kasar da muke rayuwa a ciki," inji shi.

KU KARANTA KUMA: Masana sun gargadi wasu Gwamnonin arewa a kan wani mataki da suka dauka

Yayin da yake magana a taron, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo yace gwamnatin ta jajirce wajen nagance yunwa a kasar.

Wasu daga cikin kokarin sun hada da shirin ciyar da yara yan makaranta da sauran su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel